Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Kano CP Bakori Ya Ayyana Yaki da Daba, Ya Bada Umarnin Kai Samame Kan Maboyarsu.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bada umarnin kaddamar da cikakken farmaki kan ‘yan daba a fadin jihar domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Wannan mataki ya biyo bayan babban taron tsaro da aka gudanar ranar Juma’ar da ta gabata da ya hada manyan jami’an tsaro daga sassa daban-daban na jihar.
CP Bakori ya ce gwamnatin jihar ba za ta lamunci ayyukan daba ba, kuma ya umarci jami’an sa da su kai samame a dukkan maboyar ‘yan daba.
Haka zalika, ya roki al’umma da su ba da hadin kai ta hanyar bada bayanai a kan lokaci don taimakawa rundunar tsaron.









