An garzaya da Wani limamin masallaci sashin bayar da agaji gaggawa dake asibitin Murtala, sakamakon Zargin da ake yi na matarsa ta buga masa Dutse akansa.
Lamarin ya Faru ne a unguwar Zango Yar’adu’a Kwatas dake karamar hukumar Ungoggo a Jahar Kano.
Dan uwan limamin, Mallam Zakariya, ya shaida wa wakilin Aksammedia, cewa tunda aka kai shi, Asibiti bai San waye akansa ba.
Sai dai ya ce daman matar limamin a wasu lokutan ta kan nuna kamar akwai matsalar kwakwalwa akan ta.
Abdullahi Adamu, shi ne makoncin limamin ya shaida wa manema labarai cewa suna cikin gida da sassafe aka fada mu su faruwar lamarin, inda suka garzaya da shi wajen jami’an Yan Sandan Zango sannan aka tafi da shi zuwa asibitin Murtala Muhammed sashen bayar da agajin gaggawa.
” Mu na kira da mahukunta da ma su Hannu da shuni su taimaka don ceto rayuwar sa.











