Da’ace zan fallasa ire Iren Satar Zaluncin da Ganduje ya yi da yau ba zaku iya bacci ba -Gwamna Abba
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya soki tsohon gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, inda ya zarge shi da gaza aiwatar da muhimman ayyukan raya jiha a tsawon shekaru takwas na mulkinsa tare da barin baitulmalin jihar fanko.
Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis yayin rabon takardun dindindin na aiki ga malamai 4,315 a karkashin shirin Better Education Service Delivery for All (BESDA).
A cewar Abba Yusuf:
“Sun lalata Kano. Sun wawure kuɗin ku ba tare da ayyukan ci gaba ba. Idan na fallasa abin da suka aikata, ba za ku iya yin barci ba.”
Ya kara da cewa gwamnatin Ganduje ta zalunci malamai, ma’aikata da masu ritaya, ta kuma rika sayar da takardun aikin gwamnati ga malamai.
“Idan a zamaninsu ne, da sai dai a sayar muku da waɗannan guraben aiki. Amma yau babu wanda ya biya ko kobo,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta gaji jihar da asusun gwamnati da bai kai ko dubu goma ba – N9,075 ne kacal a lokacin da aka mika mana mulki.












