Mataimakiyar Gwamnan Jihar Farfesa Kaletapwa Farauta ta bayyana haka ga manema labarai, lokacin mika yaran da aka ceto ga iyayen su.
Farauta ta bayyana takaicinta da lamarin, yayin da take jinjinawa rawar da hukumomin tsaro irin su Ƴansanda da DSS da kuma NSCDC suka taka wajen gano yaran da aka yi safarar su daga jihar, aka kuma sayar da su.
Mataimakiyar gwamnan ta bayyana kama dillaliyar sayar da yaran wadda ake kira Ngozi Abdulwahab, tare da sanar da cewar an sayar da kowanne yaro guda ne akan tsakanin naira 800,000 zuwa miliyan 1,700,000.
Farauta ta ce wadda ake zargin na da shago ne a unguwar Jambutu dake Yola ta Arewa, inda take yaudarar yara da shi.
Mataimakiyar gwamnan daga bisani ta mika yaran ga iyayen us tare da ba su tallafin naira 100,000 da kuma kayan abinci.












