Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa zaɓen cike gurbi na majalisar wakilai a mazaɓar Kaura Namoda ta Kudu a jihar Zamfara bai kammala ba saboda dalilai na doka da kuma adadin katin zaɓe da ke hannun masu kada kuri’a.
Baturen zaɓen mazaɓar, Lawal Sa’adu daga Jami’ar Tarayya da ke Gusau, ne ya bayyana haka a lokacin da yake sanar da soke sakamakon rumfunan zaɓe na Sakajiki da Kambarawa.
Ya ce a wuraren da abin ya shafa an yi rajistar katin zaɓe 5,446, amma adadin masu katin da ke hannun jama’a bai wuce 3,265 ba.
A cewar sa, jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 7,001, yayin da PDP ta samu ƙuri’u 5,339, inda ake da ratar ƙuri’u 1,662. Sai dai ya ce wannan ratar ta yi ƙasa da adadin katin da ke hannun masu zaɓa a rumfunan da aka soke, abin da ya sanya zaɓen ya kasance wanda bai kammala ba.
Hukumar zaɓen ta kafa hujja da dokar zaɓe ta 2022, musamman sashe na 24 (2 & 3), sashe na 47 (3) da kuma sashe na 51 (2), wacce ta tanadi cewa zaɓe zai kasance bai kammala ba idan ratar ƙuri’un da mai nasara ya samu ba ta haura adadin katin da ke hannun jama’a
Sakajiki: Rumfunan zaɓe biyu, inda aka yi rajistar 1,357, masu katin a hannu 1,298.
Kambarawa: Rumfunan zaɓe uku, inda aka yi rajistar 4,088, masu katin a hannu 1,964.
Sa’adu ya bayyana cewa zaɓen zai ci gaba da kasancewa a matsayin wanda bai kammala ba har sai an sake gudanar da zaɓe a waɗannan wurare.
INEC ta ce za ta sanar da ranar da za a sake gudanar da zaɓe a Sakajiki da Kambarawa a wani lokaci nan gaba










