Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da cewa hare-hare da wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai a Jihar Benue sun haddasa mummunar matsala, inda aka raba iyalai 1,069, mutane 6,527 da suka haɗa da mata masu shayarwa, mata masu juna biyu da tsofaffi da muhallansu
A wani saƙo da ta wallafa a dandalin X a ranar Litinin, NEMA ta bayyana cewa hare-haren na baya-bayan nan ya faru ne da safiyar Asabar a ƙauyen Yelewata da ke cikin Ƙaramar Hukumar Guma, inda wasu ƴan bindiga suka kai wa mazauna hari, suka kashe da jikkata mutane da dama
Yansanda Sun Cafke Matasa 51 Da Ake Zargi Da Fadan Daba A Kano
Hukumar ta ce har yanzu ba a fayyace adadin waɗanda harin ya shafa ba saboda yanayin rashin tsaro da kuma ƙalubalen samun shiga yankunan da abin ya shafa.
Sai dai ta ce ana cigaba da gudanar da aikin ceto da dawo da waɗanda abin ya shafa, kuma hakan zai bayar da sahihan bayanai nan gaba.
Rundunar ƴan sandan Jihar Benue ta tabbatar da harin, inda ta ce an kashe wasu daga cikin maharan a musayar wuta da jami’an tsaro.
- A halin yanzu, NEMA ta ce ana cigaba da ƙoƙarin tallafawa Jama’ar daka raba da muhallansu.









