Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ba da wa’adin sati biyu Dan jankunne ga marasa da’a dake gudanar da tambele a kafafen sada zumunta na zamani wato social media a turance.
Daurawa ya bayar da wa’adin ne jim kaɗan bayan dawowa kan mukaminsa, bayan samun fahimtar juna da gwamna Abba Kabir Yusuf.
Cikin sakon da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook mai taken jan kunne, Sheikh Aminu Daurawa yace da bata-garin, “Sati biyu kacal na baku ku tuba ko Hisbah ta murƙushe ku.”
A daren Litinin 4/3/2024 aka sasanta Sheikh Daurawa da Gwamna Abba a wani zama da Majalisar Haɗin Kan Malamai da Ƙungiyoyin Jihar Kano ta jagoranta a gidan gwamnatin jihar.
Majiya mai tushe ta shaida cewa Babban Limamin Masallacin ƙasa da ke Abuja, Sheikh Ibrahim Maƙari da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Falgore, suna daga cikin waɗanda Gwamna Abba ya turo domin su yi masa bikon Sheikh Daurawa.
Murabus din Sheikh Daurawa daga shugabancin Hisbah dai ya bar baya da ƙura, inda aka yi ta kiraye-kiraye da roƙon sa ya koma ya dora a kan nasarorin da hukumar ta samu a ƙarkashin jagorancinsa, musamman a ɓangaren yaƙi da badala.
A Juma’ar da Sheikh Daurawa ya sauka, wasu ƴan daudu sun kai wa jami’an Hisbah hari a ofishinsu a Kano, baya ga wata dabdala da suka gudanar tare da mata masu zaman kansu domin murnar saukar malamin.
Tun ranar Alhamis a lokacin taron da Gwamna Abba ya yi da malaman Jihar Kano kan shirye-shiryen azumin Ramadan da ke tafe ne gwamnan ya soki yadda jami’an Hisbah ke kai samame a matattaran bata-gari suna yi wa bata-garin ɗiban karan mahaukaciya, ba maza, ba mata, ake ta ce-ce-ku-ce.
Wasu dai na ganin gwamnan ya yi daidai domin gyara ne ya yi wa hukumar ayyukanta, saboda jami’anta suna wuce gona da iri.
A gefe guda kuma wasu na ganin gwamnan ya yi katobara, kuma kalaman nasa tamkar kariya ce ga masu ayyukan masha’a a jihar, da kuma fifita su a kan malamin, wanda suke ganin an ci mutuncinsa, musamman ganin cewa malamin ba ya wurin kuma gwamnan na da ikon kiran sa ya yi masa gyara ba a bainar jama’a ba.
Hasali ma tun watanni uku da suka wuce da abin ya faru Sheikh Daurawa ya sanar cewa sun gyara kuskuren, har sun hukunta waɗanda suka aikata ba daidai ba.
Washegari, Juma’a da sassafe Sheikh Daurawa ya sanar cewa ya sauka da muƙamin, saboda kalaman gwamnan, sannan ya yi wa gwamnan da gwamnatinsa fatan alheri da samun nasara, matakin da wasu ke ganin ya yi daidai.
Wasu dai na zargin subul-da-bakan gwamnan ya yi na da alaka da dambarwar shahararriyar ƴan tiktok Murja Kunya, wadda ta tayar da ƙura bayan an fitar da ita daga gidan yarin da kotu ta ba da umarnin ta bayan hukumar Hisbah ta gurfanar da ita kan zargin lalata tarbiyya tare da koya wa yara karuwanci da kuma razana jama’a.
Da dama daga cikin jama’a na zargin akwai hannun gwamnatin jihar Kano wajen fitar da Murja daga gidan yarin ta barauniyar hanya, zargin da gwamnatin ta musanta.









