Daga Hassan Umar Gwammaja
Hukumar NYSC ta tabbatarwa da ƴan yi wa ƙasa hidima cewa za a ƙara kuɗin alawus na N33,000 da ake biyan su a duk wata da zarar gwamnatin tarayya ta aiwatar da sabon tsarin albashi mafi ƙarancin.
Shugaban hukumar NYSC, Yusha’u Ahmed, shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da ya ziyarci jihohin Kebbi da Sokoto domin jawabi ga ƴan yiwa ƙasa hidima na 2024 Batch ‘B’ na biyu a sansanonin horaswa na jihohin biyu.
Ya bayyana cewa gudunmawar da ƴan yi wa ƙasa hidima ke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin ƙasa yana da matuƙar muhimmanci, inda ya jaddada cewa ya kamata ƴan yiwa kasa hidima su yi amfani da shekarar hidimar su wajen bunƙasa kansu da shirya wa kansu ingantacciyar makoma.
Shugaban hukumar ya ce, “Aƙalla, ku koyi sana’a yayin da kuke sansanin, kuma bayan kammala tsarin horaswa, dama bayan fita daga sansanin.
Ku yi ƙoƙarin koyon sana’ar da za ta ba ku damar ƙirƙirar ayyukan yi da ɗaukar ma’aikata maimakon neman aikin yi. Muna da tsofaffin ƴan yiwa ƙasa hidima da yawa a faɗin ƙasar da suke yin nasara a cikin sana’o’in su daban-daban a yau.”
“Hukumar NYSC ta haɗa hannu da ƙungiyoyi masu nagarta da yawa kamar Babban Bankin Najeriya (CBN), Bankin Masana’antu (BOI), Unity Bank, Access Bank, da gidauniyar NNPC da sauransu, waɗanda ke taimakawa wajen ba da rance da tallafi ga ƴan yiwa ƙasa hidima.”
Ya tabbatar musu da cewa za a tabbatar da tsaron lafiyar su a duk tsawon shekarar hidimar su.












