Guda daga cikin Yan media Datti Assalafi, ya gabatar da Karin shawarwari ga fitaccen Dan uwan sa Dan media wata Dan Bello, inda Yace “Wallahi da kyakkyawan zuciya nake baka shawara akan yadda zaka kare kanka, kar ka bari ‘yan zuga su sa ka sakankance, ni victim ne na masu cin amanar Nigeria, ina baka shawara ne from the practical experience da nayi perceiving daga garesu, masu karin magana sukace wanda yake zaune a karkashin bishiya yafi kowa sanin karfin iska da take kadawa
Na ga wasu ‘yan zuga suna cewa ba abinda zai faru da kai, ai kafi karfin maciya amana, ba zasu iya maka komai ba, ka cigaba da gudanar da lamuranka kawai, suna tare da kai
To shine nake son na ja hankalinka akan ‘yan zuga, suma suna da nasu hatsarin, kar ka biye musu, Gwamnati tana da karfi, ba wanda yafi karfin Gwamnati sai Allah kadai
Da yawa daga cikin wadanda zasu zugaka sune zasu dawo suna maka dariya idan wani abu na jarrabawa ya sameka, har ma su aibataka, kuma ba zasu iya tsinana maka komai ba, babu abinda zai ceceka sai gaskiyarka
Ka cigaba da Gwagwarmaya Dan Bello bisa tsantsar gaskiya, amma kayi taka tsantsan sosai, ka dauki matakin kariya masu tsauri wa kanka, sannan ka dabbaka shawarwarin da na baka, zasu maka tasiri Insha Allah
Ya Kara da cewa Malam Dan Bello kamar yadda na baka shawara a farko a bayyane saboda ta amfani wasu ‘yan gwagwarmaya, ina so na kara baka shawara a karo na biyu
Dan Bello ka sani mutum baya zama cikakken dan Gwagwarmaya sai ya hadu da kalubale daga azzalumai, kalubalen da zaka iya fuskanta sune kamar haka
(1) Kamu da dauri
(2) Cutarwa
(3) Cin amana
(4) Sharri
(5) kisa
Dan Bello ka sa a ranka cewa daya cikin biyar din abinda na lissafa zai iya samunka (ina fatan Allah Ya baka cikakken kariya)
Wallahi da kyakkyawan zuciya nake baka shawara akan yadda zaka kare kanka, kar ka bari ‘yan zuga su sa ka sakankance, ni victim ne na masu cin amanar Nigeria, ina baka shawara ne from the practical experience da nayi perceiving daga garesu, masu karin magana sukace wanda yake zaune a karkashin bishiya yafi kowa sanin karfin iska da take kadawa
Na ga wasu ‘yan zuga suna cewa ba abinda zai faru da kai, ai kafi karfin maciya amana, ba zasu iya maka komai ba, ka cigaba da gudanar da lamuranka kawai, suna tare da kai
To shine nake son na ja hankalinka akan ‘yan zuga, suma suna da nasu hatsarin, kar ka biye musu, Gwamnati tana da karfi, ba wanda yafi karfin Gwamnati sai Allah kadai
Da yawa daga cikin wadanda zasu zugaka sune zasu dawo suna maka dariya idan wani abu na jarrabawa ya sameka, har ma su aibataka, kuma ba zasu iya tsinana maka komai ba, babu abinda zai ceceka sai gaskiyarka
Ka cigaba da Gwagwarmaya Dan Bello bisa tsantsar gaskiya, amma kayi taka tsantsan sosai, ka dauki matakin kariya masu tsauri wa kanka, sannan ka dabbaka shawarwarin da na baka, zasu maka tasiri Insha Allah
Allah Ya taimaka, Ya karemu daga sharrin maciya amanar Nigeria
Daga Datti Assalafi