• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yadda Najeriya ta ci tarar kamfanin meta Dala Miliyan 220 bisa wani Dalili

aksam by aksam
July 20, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
472
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cin kamfanin Meta tarar dala miliyan 220, inda ta ce binciken da ta gudanar ya gano an saba dokokin kare bayanai na kasar lokuta da  yawa a shafukan Facebook da WhatsApp.

A wata sanarwa da Hukumar kare hakkokin masu sayayya ta FCCPC ta fitar, ta lissafa hanyoyi biyar da kamfanin Meta ya saba dokokin bayanai a kasar da ke yammacin Afirka, ciki har da ta hanyar musayar bayanan ‘yan Najeriya ba tare da izininsu ba, nuna wariya da sauransu.

Nan take dai mai magana da yawun kamfanin Meta bai maida martini kan bukatar yin bayani a kan batun ba.

Najeriya, kasar da ta fi yawan al’umma a nahiyar Afirka, ta na da manyan rukunonin da aka fi amfani da intanet a duniya inda mutane miliyan 154 suka yi rijistar amfani da intanet a shekarar 2022, a cewar hukumar kididdiga ta kasar.

Duk da yawan masu amfani da intanet a kasar, kamfanin Meta ya kasa bin dokokin kariyar bayanai ta Najeriya.

Bayan tarar dala miliyan 220, umurnin hukumar ya bukaci kamfanin Meta ya kiyaye dokokin cikin gida na Najeriya ya kuma daina “ci da gumin ‘yan Najeriya masu amfani da shafukan Facebook, Whatapp, da Instagram

A watan Mayun shekarar 2021 ne aka fara binciken saba ka’idodjin a lokacin da hukumar ta bude wani bincike kan wasu sabbin manufofin amfani da shafin WhatsApp. Ta kuma sanar da kamfanin Meta sakamakon binciken, lamarin da ya sa daga baya kamfanin ya gabatar da kudurin yin garambawul wanda ya kasa magance matsalolin farko, a cewar sanarwar.

Tags: Aksam radioaminiyaArewa radioBbchausaDAILY TRUSTfreedom radioKadaura24punch NewspaperrfihausaSamoaSolacebasetrthausaVanguard newspapervoahausazanga-zanga
Share189Tweet118SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Sibul da baka ya saka wani magidanci zubar da hawaye a gaban kuliya yayin yanke hukunci

Next Post

Mai Martaba Sarkin Kano; Na Goma 15 Alhaji Aminu Ado Bayero Ya Halice Taron Khatamar Karatun Al’qur’anin Mai Girma Tare Da Yiwa Kasa Addu’ar Samun Zaman Lafiya

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan
LABARAI

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

by aksam
May 4, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano
LABARAI

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A  Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga  Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC
LABARAI

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC

by aksam
May 3, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Zargin badakala da dukiyar kasa CBN ya kori maaikatansa fiye da 100

April 11, 2024
Majalisar wakilai ta nemi Tinubu ya dakatar da yarjejeniyar SAMOA da zata Ba shi damar samun Dala 150b

Yanzu-yanzu majalissar wakilai ta janye kudurin da ta shigar Akan sabon taken Najeriya

August 14, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media