Rundunar sojin ta fitar da jerin hotunan jami’anta da aka yi wa kisan gilla
Sojoji 17 aka yi wa kisa gilla a jihar Delta da ke kudancin Nijeriya. Hoto: Rundunar sojin Nijeriya
Rundunar sojin Nijeriya ta fitar da jerin hotunan jami’anta da aka yi wa kisan gilla a jihar Delta da ke kudancin Nijeriya a makon jiya.
Ta wallafa hotunan nasu ne a shafinta na X a yau Litinin da maraice, inda ta sake bayyana jimamin rashin da ta yi, wanda take zargin wasu ɓata-gari da aikata shi.
Sanarwar rundunar na zuwa ne a daidai lokacin da take zargin al’ummar ƙauyen Okuama na Jihar Delta da hannu a kitsa lamarin, tare da yaɗa farfaganda don “rufe aika-aikar da suka yi”.
Wannan lamari ya faru ne a a ranar Alhamis, lokacin da sojojin suka kai ɗauki a wani rikicin ƙabilanci da ke faruwa tsakanin al’ummomi biyu na yankin.












