Hadakar kungiyoyi masu goyon bayan jam’iyyar APC ta bayyana cewa Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinbu yana da manufa mai kyau ga ‘yan Najeriya
Farfesa Mohammed Kailani, shugaban gamayyar kungiyoyin ya shawarci ‘yan jam’iyyun adawa su bada gudunmawa su yi amfani da dukiyarsu don ceto ‘yan Najeriya daga talauci
Kailani, har ila yau, ya yi kira ga ‘yan Najeriya su bai wa shugaban kasan hadin kai da goyon baya domin ya samu ya cimma manufofinsa na alheri a gare su
Kailani, wanda ya nemi a goyawa shugaban kasar baya, ya kuma yi kira ga ‘yan adawa da su bar shi ya gudanar da mulki su daina masa katsa-landan.
“Shugaban kasa na da manufofi na yakar duk wani abu da zai hana walwalar al’ummar kasar nan.










