• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kalli barazanar da Amurka ta yiwa kasar Niger akan alakarta da Rasha da Iran

aksam by aksam
March 19, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Hedkwatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta sanar da cewa tawagar Amurka ta je Yamai a makon jiya ne domin nuna damuwarta dangane da alaƙar da ke tsakanin Nijar da Rasha da Iran, ko da yake daga bisani Nijar ɗin ta yanke ƙawancen soji da ke tsakaninta da Amurka mai soji kusan dubu a ƙasar.

Pentagon ta ce a halin yanzu tana nazari kan batun mafita dangane da wannan lamarin.

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

A sanarwar da sojojin na Nijar suka fitar a ranar Asabar, sun ce sun yanke duk wata hulɗa da ta danganci haɗin-kai ta fannin soji da ƙasar Amurka “nan-take”.

Mai magana da yawun Pentagon Sabrina Singh ta ce “Tawagar Amurka ta je can ne domin nuna damuwa kan wasu lamura… Mun damu kan hanyar da Nijar ta ɗauka.”

Yauƙaƙa dangantaka da Rasha

Tun bayan kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum da sojoji aka yi a watan Yulin 2023, sojojin na Nijar suka ɗauki matakin fatattakar sojojin Faransa da na wasu ƙasashen Turai daga ƙasar tare da sanar da ficewarsu daga ECOWAS.

Kamar sauran sojojin da ke mulki a Mali da Burkina Faso, ita ma ƙasar ta ƙara yauƙaƙa dangantakarta da Rasha.

Wasu manyan jami’an gwamnatin Rasha daga ciki har da Yunus-bek Yevkurov, wanda shi ne mataimakin ministan tsaron Rasha sun kai ziyara Nijar inda suka haɗu da sojojin da ke mulkar ƙasar.

Firaiministan gwamnatin ta Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya kai ziyara Iran a watan Janairu.

‘Zargi maras tushe’

A sanarwar da suka fitar a ranar Asabar, sojojin na Nijar sun yi watsi da zargin da Amurka ta yi kan cewa Nijar ɗin “ta saka hannu kan yarjejeniya ta sirri da Iran game da ma’adinin Uranium.”

Sai dai Singh ba ta yi wani ƙarin haske ba dangane da batun zargin alaƙar Nijar ɗin da Iran.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Jerin jami’o’i 20 mafiya inganci a Afrika

Next Post

Rundunar sojin ta fitar da jerin hotunan jami’anta da aka yi wa kisan gilla

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan
LABARAI

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

by aksam
May 4, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano
LABARAI

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A  Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga  Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC
LABARAI

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC

by aksam
May 3, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Wani Farfesa ya fadi abin da zai faru idan Tinibu ya gaza shawo kan tsadar rayuwa a Najeriya

Binciken Dala 6m da aka sata da sahanun Buhari ya canza salo

February 20, 2024
Shugaba Tinubu ya jagoranci sulhunta Wike da Gwamna Fubara da ya gaji shi

Shugaba Tinubu ya jagoranci sulhunta Wike da Gwamna Fubara da ya gaji shi

December 18, 2023
ADVERTISEMENT

Trending.

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media