DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
Da Safiyar yau Litinin ne, Ƙungiyar Masu Sana’ar Garuwa Suka tsunduma yajin aikin gargadi na kwana biyu a Jihar Kano, biyo bayan cin zarafi da ake musu na karbar haraji a karamar hukumar Ungogo.
Masu Sana’ar Garuwan sunce lamarin yana faruwa ne a kan iyakar kananan hukumomin Nasarawa da Ungogo, a titin da aka fi Sani da titin Rimin Keɓe.
Up. L
Masu ruwan sun bayyana cewa mutanen dake tare su a hanyar na karɓar naira ɗari biyar a hannun su, idan kuma suka gaza biya sai su ƙwace musu Jarakuna ko kuma su ci zarafin su.
Mustafa Ghali ya na cikin ‘Yan Garuwan da suka tafi yajin aikin, ya ce sun ɗauki matakin ne a sakamakon yadda wasu Mutane da basu san ko su waye ba suke tare su suna karɓar naira ɗari biyar a gurinsu, idan kuma basu bayar ba sai su ɗebe musu jarkoki.
Shima Muhammad Shehu Usman ya ce, gani ake kuɗi suke tara wa, bayan ba’a san nawa suke siyan Ruwan a gidan Ruwa ba, ba’a san nawa suke biyan kuɗin kura ba, Kuma ba’a san nawa suke samu ba, adan haka suka tafi yajin aikin domin yanyo hankalin mahukuntan su bincika lamarin.
Matakin zai Shafi Unguwanni Rimin keɓe, Tudun Murtala, Gama dama yankin Birget, Yankunan da suka dogara kacokan akan masu Sana’ar Garuwan duba da yadda suka shekaru masu yawa suna fama da matsalar Rashin Ruwan da suke amfani dashi a dukkan harkokin su na yau da kullum.











