Daga: Hassan Umar Gwammaja
A ranar Asabar 10 ga watan Janairu, 2026 ne aka gudanar da Walima Saukar tare da Haddar Karatun Al’qur’ani Mai Girma na daliban maza da mata karo na takwas (8)
Dayake gabatar ta jawabin Na’ibin Limamin Masallachin Juma’a Na Tunawa da Abubakar Sadik NDC Unguwar Kaje Kaduna Malam Zubairu Muhammad Khamis ya farane da bayyana fa’idar haddar Al’qur’ani Mai Girma dare da yin aiki da shi
Shi kuwa, Ustaz Mika’ilu Umar shi ne shugaban makarantar ta Ihya’is Sunnah dake Kaduna ya godiwa wadanda suka halarci wajan taron bikin Saukar












