Mai bincike na musamman da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya nada ya bukaci hukumar yan sanda ta kasa da kasa wato interpol ta sanya ido kan wani ma’aikacin babban bankin Najeriya CBN da wasu mutum biyu.
Matakin ya zo ne bayan bankado wasu takardun bogi da sunan tsohon shugaba Muhammadu Buhari na zargin satar dala miliyan shida da dubu dari biyu kafin babban zaben 2023.
Tun farko wani tsohon sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha ya shaida wa babbar kotu a Abuja kamar yadda jaridar DailyTrust ta rawaito cewa takardun da aka yi amfani da su wajen biyan masu sa ido a zaben dala miliyan shida da dubu dari biyu na boge ne.
Tsohon sakataren gwamnatin Najeriyar ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a matsayin shaida ta hudu a shari’ar da ake yi kan tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, bisa zargin karkatar da dala miliyan shida da dubu dari biyu.











