• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kotun PRP Dake Jihar Kano Ta Tisa Keyar Murja Ibrahim Kunya Zuwa Gidan Gyaran Hali

aksam by aksam
February 13, 2024
Reading Time: 1 min read
1
Home KOTU
ADVERTISEMENT
473
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA

An gurfanar da shahararriyar yar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya, a gaban kotun shari’ar addini musulinci dake zaman ta a unguwar Gama PRP Kano, bisa zarginta da aikata laifukan kawo batagari cikin dare , aikata badala, tada hatsaniya da kuma razanarwa wanda yin hakan ya saba da sashi na 341, 275 da 227 na kundin SPCL kamar yadda jarida Aksam Media ta rawaito

RelatedPosts

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar (ADC) Na Kasa

Kotun Koli ta yanke hukuncin kan rikicin jam’iyyar PDP

Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta cafke ta tare da gurfanar da ita a gaban kotun, bayan ta karbi korafe-korafen mazauna unguwar Tishama a karamar hukumar Nasarawa Kano.

Bayan gurfanar da ita a gaban kotun,an karonta mata kunshin zargin, inda ta musanta dukkan tuhumar da ake yi mata.

Lauyan dake kare wadda ake tuhumar Barista Aliyu Umar , Ya roki kotun ta bayar da belin ta, dogaro sashi 35 da 36 na dokokin kasa , da kuma sashi na 168, 172 da 173 na kundin SPCL.

‘’ A sanya ta a hannu beli saboda hurimi ne na kotun , sannan idan ta bayar da belin tab a zata gudu ba, ko aikata wani laifi da ya saba da doka’’ Barista Aliyu Umar’’.

Lauyan gwamnatin jahar Kano da ya wakilci kwamishinan shari’a na jahar Kano, Barista Aminu Umar bai yi suka akan rokon wadda ake tuhumar ba.

‘’ Ba mu da suka akan wannan roko domin bayar da beli hurimin kotu ne’’ lauyan Gwamnatin Kano’’.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed , ya bayar da umarnin ci gaba da tsare wadda ake zargin a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 22 ga watan fabarairun 2024.

Share189Tweet118SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Yau Ce Ranar Radiyo Ta Duniya:- Ko Wace Godinmawa Radiyo Take Baku A Cikin Al’amuran Rayuwarku ?

Next Post

Tsadar rayuwa, wata kungiyar yarbawa ta nemi Tinibu yayi murabus

aksam

aksam

RelatedPosts

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar  (ADC) Na Kasa
KOTU

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar (ADC) Na Kasa

by aksam
April 30, 2026
Yau Ake Sa Ran Kotun Koli Ta Najeriya Zata Yanke Hukunci A Yau Kan Rikicin Shugabancin  Jam’iyyar ADC A Matakin Kasa
KOTU

Kotun Koli ta yanke hukuncin kan rikicin jam’iyyar PDP

by aksam
April 30, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi
KOTU

Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi

by aksam
April 22, 2026
Yau Ake Sa Ran Kotun Koli Ta Najeriya Zata Yanke Hukunci A Yau Kan Rikicin Shugabancin  Jam’iyyar ADC A Matakin Kasa
KOTU

Yau Ake Sa Ran Kotun Koli Ta Najeriya Zata Yanke Hukunci A Yau Kan Rikicin Shugabancin Jam’iyyar ADC A Matakin Kasa

by aksam
April 22, 2026

Comments 1

  1. Muhammad Yusuf Muhammad says:
    2 years ago

    Mugunji mugun gani Allah yakaremu

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Bayan harbe gomman Yan zanga-zanga, NLC tayi martani ga rundunar Yansanda

Bayan harbe gomman Yan zanga-zanga, NLC tayi martani ga rundunar Yansanda

August 3, 2024
Yawan hadaru ya tilastawa jiragen yakin sojin saman Amurka rage tashi

Yawan hadaru ya tilastawa jiragen yakin sojin saman Amurka rage tashi

April 29, 2023
ADVERTISEMENT

Trending.

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media