Rundunar sojin kasa ta Amurka ta bayar da umarnin dakatar da tashin dukkanin jiragen samanta na bayar da horo bayan hadarin jiragen sama masu saukar ungulu biyu da suka yi sanadiyyar mutuwar sojoji goma sha biyu.
Za a yi amfani da tsawon lokacin dakatarwar ne wajen sake nazarin matakan kiyaye hadura da kuma horo.
Sojojin Amurka na kasa guda uku ne suka rasa ransu wani guda daya kuma ya ji rauni lokacin da wasu jiragen sama biyu masu saukar ungulu samfurin Apache na rundunar sojin suka yi karo ranar Alhamis a sararin saman jihar Alaska.
Biyu daga cikin sojojin sun mutu nan take daya kuwa a hanyar kai shi asibiti rai ya yi halinsa yayin da na hudun aka ce ya tsira da raunuku, ko da yake ya samu sauki zuwa yanzu.
A dalilin wadannan haduran ne rundunar sojin kasa ta Amurkar ta sanar da cewa za ta dakatar da tashin duk wasu jiragenta na sama har sai kowane sashe ya yi wani horo na musamman na kwana daya na kauce wa hadari a cikin mako mai zuwa.
Sannan kuma za a sake duba tsarin nazarin kauce wa hadura da aikin sanya ido.
Sai dai kuma duk da wannan mataki rundunar ta ce za a ci gaba da duk wasu ayyukan amfani da jiragen saman wadanda suka zama na dole.
Amma kuma ko su ma sai wani Janar na sojin mai mukamin akalla daga Manjo Janar zuwa sama ya bayar da umarni.
Dokar ta shafi jiragen saman rundunar sojin kasa na Amurka ne kawai ba ta shafi sauran sojin kasar kamar rundunar sojin sama ko na ruwa ba.












