Wasu miyagun ƴan bindiga 3 da suka kware wajen garkuwa da mutane sun baƙunci lahira.
Lamarin ya faru ne a jihar Adamawa da ke shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.
Jaridar The Nation ta bankado cewa dakarun ƴan sanda ne suka sheƙe su a wani samame da suka kai tare da taimakon mafarauta ƴan sa’kai.
Yayin wannan samame da jami’an tsaron suka fita, sun yi nasarar ceto mutum biyu da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su, Daily Post ta ruwaito.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu.
Ya ce ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, 2024, ‘yan sanda suka ragargaji kungiyar miyagun a tsaunin Koma mai hade da garuruwan Kojoli da Karlahi na kananan hukumomin Jada da Fufore a Adamawa.
Yan sanda sun ceto mutum da aka sace Kakakin ƴan sandan ya ci gaba da cewa:
“Jiya Laraba, masu garkuwa suka kai hari a wani wurin kiwon shanu na Alhaji Jibo Karlahi inda suka tafi da Umar Jibo mai shekaru 18 da Idi Hassan mai shekaru 13 a duniya.
“Nan take rundunar ƴan sanda ta tashi tawagar ceto suka bi sawun maharan.
Daga ganin dakarunmu sai suka buɗe wuta aka fara musayar wuta. Sakamakon haka muka kashe 3 daga cikinsu.
“Amma sauran sun ari na kare ɗauke da raunukan harbin bindiga, abin farin cikin mun yi nasarar ceto mutum 2 da suka sato ba tare da an cutar da su ba.
” A cewarsa, wannan nasara na ɗaya daga cikin ƙoƙarin rundunar na magance aikata manyan laifuka da suka haɗa da garkuwa, satar shanu, fashi da sauransu a jihar.











