• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Rikicin kabilanci da Addini na kara kamari a jihar pilato

Sy lawan by Sy lawan
January 26, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Akalla mutane 43 ne suka mutu cikin kwanaki biyu da aka shafe ana tashin hankali a ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar Filato kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC hausa.

Sai dai rundunar yan sanda a jihar ta ce ta kama mutum tara da ake zargi da hannu a tashin hankalin da kashe-kashen na karamar hukumar Mangun.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Lamarin na zuwa ne bayan da sojojin Najeriya suka zargi makiyaya da kashe-kashen da kuma satar shanu.

Kakakin hedikwatar tsaron Najeriya, Janar Edward Buba ya ce an tura sojoji na musamman zuwa yankunan da rikicin ya fi kazanta domin dakile bazuwar tashin hankalin.

Wata takaddama a kan shanu ce ta janyo tashin hankalin a Filato – yankin da ake yawan samun hatsaniya mai alaka da addini da kabilanci.

Wani mutum a garin Mangu ya fada wa BBC yadda aka kashe dan’uwansa mai shekara 63 a gidansa wanda daga baya aka cinna wa wuta.

“A yanzu da nake magana, yaransa shida suna kuka. Mun yi jana’izarsa tare da wasu gawawwaki 14,” in ji shi.

Filato jiha ce da ke da cakuɗuwar al’umma musulmai da kuma mabiya addinin kirista.

Mazauna Mangu da ke da nisan kilomita 74 daga garin Jos, babban birnin jihar yanki ne da galibin mazaunansa Musulmai ne makiyaya da kirsitoci yan kabilar Mwagaful.

Wani bafulatani dan kasuwa Umar Haruna yana gida a lokacin da rikicin ya ɓarke ranar Talata, ya ce an kona masallatai bakwai da majami’u hudu da gidaje 100

Mai dakin Umar Haruna da yaransu ba sa gida lokacin da aka kai hari a gidan. Sun koma gidan ne a ranar Laraba.

“Lokacin da muka je gidan, mun ga gawarsa kone kamar dai yadda aka kone gidan. Ba mu samu yin wankan gawa ba saboda yadda gawar ta dagargaje,” kamar yadda dan’uwansa ya bayyana.

Dagen Emmanuel Bello, daga kabilar Magwaful ya ce ya ga gawawwaki yashe a kan titi an kuma kona gidaje.

“Akwai wasu mutane da aka kashe aka kuma boye gawawwakinsu, muna ci gaba da kokarin nemo su,” kamar yadda ya fada wa BBC.

Tashin hankalin ya soma ne bayan da wata saniya mallakin makiyaya ta tsere inda ta hau kan titi lamarin da ya fusata al’ummar Mwagaful.

An sa dokar hana fita – ba dare da rana amma matakin bai dakatar da tashin hankalin ba.

Mutane a yankin sun ce an tura sojoji zuwa Mangu amma sun tsaya a manyan tituna sannan kuma ba a ga keyarsu a yankunan da ake hare-haren ramuwar gayya ba.

Fiye da mutum 100 ne suka rasa rayukansu a hare-hare daban-daban da suka faru a wani bangare na jihar ta Filato daga jajiberin Kirsimet

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Kalli yadda wasu masu garkuwa da mutane suka hadu da ajalin su a kokarin sace wasu mutane

Next Post

Промокоды и фриспины Вавада для игроков в 2026 году

Sy lawan

Sy lawan

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Shugaban Iran, Ministan Harkokin Wajen Kasar, Da Wasu Mutane 7 Sun  Kwanta Dama A Hatsarin Jirgin Sama

Shugaban Iran, Ministan Harkokin Wajen Kasar, Da Wasu Mutane 7 Sun Kwanta Dama A Hatsarin Jirgin Sama

May 20, 2024
Abin takaici, yan bindiga sun dauke Ango da Amarya

Wasu Yan bindiga sun yi barazanar kashe mutane bakwai bayan idan ba’a biya musu bukatar su ba

February 1, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media