Wasu ƴan bindiga da suka sace mutum bakwai a yankin Kuduru na ƙaramar hukumar Bwari a Abuja, sun buƙaci a ba su N290m a matsayin kuɗin fansa.
Ƴan bindigan dai sun sace mutanen ne a ranar 28 ga watan Disamban 2023.
Sauran abubuwan da ƴan bindigan suka nema kuma sun haɗa da magunguna da kayan abinci kafin su sako mutanen da suka yi garkuwa da su, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Mutanen da aka sace ɗin dai sun haɗa da wata mata mai juna biyu, yara uku da manyan mutane huɗu, waɗanda yanzu sun shafe wata ɗaya da kwana huɗu a hannun ƴan bindigan.
Jaridar TheCable ta ruwaito cewa tun da farko ƴan bindigan sun buƙaci a ba su N500m, kafin su sako mutanen. Menene buƙatun ƴan bindigan?
Wani shugaba a yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ƴan bindigar sun yi barazanar kashe mutum biyu daga cikin mutanen bawan matukar ba a biya musu buƙatunsu kan lokaci ba.
Ya ce masu garkuwan sun kuma buƙaci kayan abinci da magunguna da barguna da rigunan sanyi.
Cikin lafazinsa yace: “Sun yi mana magana mu kawo N290m domin su sako su ko kuma su kashe mutum biyu daga cikinsu. Muna da mace mai ciki da yara uku a cikinsu











