Sabon Shugaban Shugabancin Kungiyar Matuka Motocin Haya ta Kasa Reshen Tashar Malam Kato,ya bayyana cewa, a shirye yake wajen ciyar da Kungiyar da harkokin Sufuri gaba a jihar Kano.
Zabbaben Shugaban Kungiyar na Malam Kato Bus 9 Alhaji Kabiru Yahaya ne ya bayyana haka a lokacin Zantawa da Manema labarai a ofishinsa dake Tashar ta Malam Kato anan Kano.
Shugaban Kungiyar yace,ya zo da kyawawan shirye _shirye da za su inganta rayuwar matasa musamman Direbobi da suke sana’ar tukin Motocin Haya domin su kasance masu dogaro da Kawunansu.
Yace, Kasancewar akwai rashin ayyukan yi a Kasar nan ciki har da jihar Kano,ya sanya wannan sabon Shugabancin Kungiyar ta (NURTW)ta yi aniyar ganin ta hada hannu da Gwamnatin jihar Kano da hadin gwiwar da Ma’aikatar Sufuri wajen Nemowa ‘ya’yanta Motocin da za rika aiki da biyan Kudaden a hankali domin su Mallaki ta su don dogaro da kawunansu da ciyar da iyalansu.
Kabiru Yahaya ya bukaci Gwamnatin jihar Kano da ta rabawa ‘ya’yanta Motocin Haya za su samu damar mallakar nasu a matsayin ba da lamani karkashin jagorancin Unguwar Kungiya.










