Sanata Godswill Akpabio ya katse hutun majalisar dattawa, ya kira taron gaggawa kan muhimmin batun da ya shafi ƙasa baki ɗaya
Magatakardar majalisar dattawa, Chinedu Akubueze ne ya bayyana haka a wata sanarwar da ya aike wa sanatoci ranar Litinin, 29 ga watan Yuli
Taron zai gudana ne ranar Laraba, 31 ga watan Yuli, 2024 kwana ɗaya tal gabanin ranar fara zanga-zangar adawa da tsare-tsaren Bola Tinubu
Sanarwar tace “ya ku masu girma sanatoci, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Obot Akpabio, GCON, ya ba da umarnin a kira taron gaggawa na majalisar ranar Laraba, 31 ga watan Yuli da ƙarfe 12:00 na rana.
“Ana bukatar sanatoci su yi duk shirye-shiryen da suka dace domin halartar taron domin za a tattauna batutuwan da suka shafi kasa ne baki daya.”









