Daga Hassan Umar Gwammaja
Al’amarin siyasa a jihar Kano ya sake daukan wani sabon salo yayin da jam’iyyar APC ta yi watsi da kudin form din takarar shugabancin kananan hukumomi da hukumar zaben Kano, wato KANSIEC, ta sanar.
Wannan batu ya ja hankulan masu fashin baki da masana harkokin siyasa, musamman ma sakamakon kalaman sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano, Ibrahim Zakari Sarina, wanda ya bayyana rashin amincewar jam’iyyar da wannan tsari.
Ibrahim Zakari Sarina ya zargi jagororin hukumar zaben da kasancewa mambobin jam’iyyar NNPP, wanda ya bayyana a matsayin dalilin da ya sa suke da shakku kan adalcin da za a yi a zaben.
A cewarsa, wannan zargi yana nuna cewa akwai rashin daidaito da rikon amana wajen shirya zaben, wanda hakan zai iya haifar da rashin gaskiya da adalci ga dukkan jam’iyyun da ke cikin takara.
APC ta bayyana cewa duk da haka, ba za su yi watsi da shiga zaben ba, amma za su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da an gudanar da zabe cikin adalci.












