• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yiwa mata kaciya na gab da zama doka a wata kasa a nan Africa

aksam by aksam
March 19, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Yan majalisar Gambia sun jefa kuri’ar da ke amincewa da soke haramci da aka yi kan kaciyar mata, kudirin da zai cire kariyar da milyoyin yara mata ke da shi bisa tsarin doka.

‘Yan majalisar da gagarumin rinjaye sun bukaci a soke haramci, inda suke aike da matsayarsu matakin kwamitoci kafin a yi zaɓen karshe nan da wata uku.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Matar Biyar kacal ake da shi daga cikin ‘yan majalisar 58, kuma masu suka na cewa maza ne ke kokarin kakabawa mata wannan tsari.

Idan daftarin ya tsallake karatu na karshe, Gambia za ta zama ƙasa ta Farko a duniya da ke cire kariyar da mata ke da shi kan yi musu kaciya.

Ɗaya daga cikin ‘yan majalisar, Almammeh Gibba – wanda shi ye kirkiro wannan daftarin, ya shaidawa BBC cewa wannan tsarin bai taba cutar da jikin wata mace ba, abu ne na al’ada, ya shafi kuma addini kuma wannan abu ne da ake yinsa tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.

Ya kuma ce mutane da dama na son ganin an cigaba da wannan al’ada.

“Akwai abubuwa na cutarwa da dama da ake yiwa jikin mata amma ba za ka ji ƙasashen yamma na magana a kai ba”.

Ƙungiyoyi kare hakkin bil adama sun ce soke haramcin wannan doka da ake amfani da ita tun 2015, zai shafe fafutikar da aka kwashe shekara da shekaru domin kare ‘yanci mata da kawo karshen yi musu kaciya.

Michele Eken mai bincike a kungiyar Amnesty International ta shaidawa BBC cewa sai da aka shafe shekaru kusan 10 kafin a yi hukunci na farko kan aikata wannan abu.

A shekarar 2023 aka hukunta mutum na farko, kuma wannan ne ya bijiro da batun neman soke dokar baki-ɗaya.

Ta ce “Amma maimakon a sake komawa gidan jiya, ya kamata a ce an karfafa dokar da kokarin ganin a cigaba da hukunta masu karyata, saboda wannan na faruwa ne bayan jarirai 8, ciki harda ‘yar kasa da shekara guda, an yiwa kaciya, kuma mata uku da aka hukunta an ci su takarar kusan dala dari biyu.

“Maimako a ce an tsaurara hukucin, sai gashi ana maganar soke dokar baki ɗaya wanda tamkar ana faɗawa yara mata cewa basu da ‘yanci”.

Wani bincike na baya-bayanan na nuna cewa kashi 73 cikin 100 na mata a Gambia anyi musu kaciya, kuma kashi 65 na wannan adadi anyi musu kaciyar ne tun suna kasa da shekara biyar a duniya.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

‘Yan Bindiga A Jihar Bauchi Sun Kashe Wani Basarake Bayan Sun Yi Garkuwa Da Shi

Next Post

Kalli Putin yadda ya cika baki ga Amurka da kawayent

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Shugaban JIBWIS na kasa Sheikh Bala Lau ya bukaci a dauki matakin Alqunutu kan wadanda suka Hana Najeriya zama lafiya

Shugaban JIBWIS na kasa Sheikh Bala Lau ya bukaci a dauki matakin Alqunutu kan wadanda suka Hana Najeriya zama lafiya

July 31, 2024
Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince;  Da Dokar Kafa Masarautu Masu Daraja Ta Biyu

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince; Da Dokar Kafa Masarautu Masu Daraja Ta Biyu

July 16, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media