DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
Lamarin ya faru ne ranar Lahadi a Dogon-Fili kusa da Katari a Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.
Karo na farko ke nan cikin fiye da wata 10 da mahara suka sace jama’a a kan titin Abuja zuwa Kaduna.
Binciken Aksam Media ya nuna cewa hari na karshe da aka kai a kan titin shi ne na ranar 1 ga watan Maris, 2023, wanda da aka sace mutum 23.
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Kwamared Shehu Sani ya sanar a shafinsa na X cewa abokansa biyu daga ’yan siyasa sun tsallake rijiya da baya a harin na ranar Lahadi.
Ya ce ’yan bindigar sun ci karensu babu babbaka na tsawon lokaci duk da cewa an girke jami’an tsaro a kan babar hanyar.
Shehu Sani ya kuma kara da cewa, “A daidai lokacin da muke tunanin mun samu kwanciyar hankali, a daren jiya (Lahadi) ’yan bindiga sun kai hari, sun dawo hanyar Kaduna-Abuja.
“Sun tare hanyar da misalin karfe 9 na dare inda suka sace mutane masu yawa a kusa da kauyen Katari.
“Abokaina biyu, dan jam’iyya mai mulki da dan adawa sun tsere daji kamar Usain Bolt
“Amma duk da an inganta tsaro a kan hanyar fiye da yadda yake a baya” In ji shi
Wani mazaunin garin Katari, Suleiman Dan Baba, ya ce da misalin karfe 9:33 na dare ne ’yan bindiga dauke da bindigogi kirar AK-47 suka fito daga daji suka tare kowane bangaren titin kuma sun dauki tsawon minti 45 a kan hanyar.
Suleiman ya sake bayyana cewa, maharan sun bude wa motocin matafiya wuta, suka fasa musu tayoyi, wanda hakan ya sa dole suka tsaya.











