• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yadda Jirgin sama ɗauke da mutane 242 yayi hatsari

aksam by aksam
June 12, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Jirgin saman Air India ɗauke da mutum 242 ya yi hatsari a Ahmedabad, babban birnin jihar Gujarat da ke yammacin Indiya, kamar yadda kafafen yada labarai da dama suka ruwaito.

A cewar rahoton, jirgin AI171 ya tashi ne daga Ahmedabad zuwa filin jirgin sama na Gatwick na Landan a lokacin da hatsarin ya faru.

RelatedPosts

Iyalan Janar Rabe sun Musanta Sanarwar Gwamnatin Katsina Kan Dalilin Mutuwarsa

Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato

Rahotanni Daga Jihar Imo Sun Bayyana Cewa Wani Magoyin Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Rasa Ransa

Jirgin ya fado ne a ginin ɗakunan kwanan likitoci jim kadan bayan tashinsa daga filin jirgin saman Sardar Vallabhbhai Patel da ke Ahmedabad a ranar Alhamis, kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar.

Kamfanin Air India ya ce fasinjojin da ke cikin jirgin da ya yi hatsarin sun hada da ‘yan kasar Indiya 169, ‘yan Burtaniya 53, da ‘yan Portugal 7, da ‘yan kasar Canada daya, matukan jirgi biyu da ma’aikatan cikin jirgi goma.

Kamfanin Air India ya fitar da wata takaitacciyar sanarwa ga manema labarai yana mai cewa “A halin yanzu, muna kan tantance cikakkun bayanai kuma za mu fitar da sakamakon abin da muka tattara da wuri.”

Shugaban kamfanin jiragen Air India, N. Chandrasekaran ya bayyana “matuƙar baƙin cikinsa” kan hatsarin.

“Babban abin da muka fi mayar da hankali a kai shi ne tallafa wa duk mutanen da abin ya shafa da iyalansu,” in ji shi a cikin wata sanarwa.

“Muna yin duk abin da za mu iya don taimaka wa kungiyoyin bayar da agajin gaggawa a wurin da kuma ba da duk goyon baya da kulawa.”

A cewar rahotannin farko, jirgin ya faɗi ne a kusa da yankin Meghani Nagar na birnin, inda bidiyon yadda abin ya faru da ke yawo a shafukan sada zumunta suka nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe daga wurin da hatsarin ya auku.

Jirgin ya tashi ne da karfe 1:38 na safe agogon kasar ya kuma fada cikin wani gini kusa da filin jirgin saman Ahmedabad da karfe 1:40 na rana.

Jami’an filin jiragen sama na Gatwick sun ce jirgin ya kamata ya sauka a birnin Landan da karfe 6.25 na yamma agogon kasar.

Hukumomin kasar sun kaddamar da aikin ceto, kuma jami’an agajin gaggawa sun garzaya wurin da lamarin ya faru.

Yayin da bayanai ake ci gaba da samun taƙaitattun bayanai, majiyoyi sun nuna cewa fasinjoji da ma’aikatan jirgin na ciki a lokacin da hatsarin ya afku.

Ana sa ran jami’an hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama (DGCA) za su gudanar da cikakken bincike kan musabbabin hatsarin.

Shaidu da ke kusa da filin jirgin sun ce sun ji ƙarar fashewar wani abu mai ƙarfi kafin daga bisani jirgin ya faɗi.

Gwamnatin Gujarat ta ba da tabbacin daukar matakin gaggawa tare da tallafa wa wadanda lamarin ya shafa.

“Mun yi matuƙar kaɗuwa da jin labarin lamarin jirgin AirIndia na Ahmedabad-London a kusa da filin jirgin saman Ahmedabad,” in ji Yusuf Pathan, tsohon dan wasan cricket kuma dan majalisar dokokin Indiya, a shafin X.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Kwamishinan Jinkai Da Walwallar Jama’a Comred Markus Yunana Barda Ya Aika Da Sakon Barka Da Sallah Ga Gwamna Uba Sani, Mai Martaba Sarkin Jama’a Da Kuma Sauran Al’umma Musulmi

Next Post

Kocin Man City ya shiga sahun fitattun Mutanen dake goyon bayan Palastinawa

aksam

aksam

RelatedPosts

Iyalan Janar Rabe sun Musanta Sanarwar Gwamnatin Katsina Kan Dalilin Mutuwarsa
Uncategorized

Iyalan Janar Rabe sun Musanta Sanarwar Gwamnatin Katsina Kan Dalilin Mutuwarsa

by aksam
June 15, 2026
Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato
Uncategorized

Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato

by aksam
June 2, 2026
Rahotanni Daga Jihar Imo Sun Bayyana Cewa Wani Magoyin Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Rasa Ransa
Uncategorized

Rahotanni Daga Jihar Imo Sun Bayyana Cewa Wani Magoyin Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Rasa Ransa

by aksam
May 31, 2026
Zafin Rana Ya Hallaka Mutum 16 A Indiya
Uncategorized

Zafin Rana Ya Hallaka Mutum 16 A Indiya

by aksam
May 31, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Kwamitin Fadakar Da Al’umma Mahimmanci Mallakar Katin Zabe Ya Ziyarci Shugaban Hukumar Zabe Na Jihar Kano

Kwamitin Fadakar Da Al’umma Mahimmanci Mallakar Katin Zabe Ya Ziyarci Shugaban Hukumar Zabe Na Jihar Kano

August 23, 2025
A shirye muke wajen ganin kananan hukumomi sun dawo cikin hayyacinsu,

Gwamnan Kano Ya Bada Wa’adi Da Sharadi Domin Sauke Wasu Kwamishinoni

February 14, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media