Duk da cewa an daɗe ana ganin cewa dakarun Najeriya tare da hadin gwiwar ƙasashen makwabta sun raunana ƙungiyar Boko Haram, hare-haren da ƙungiyar ke kai wa a Najeriya sun ƙaru sosai a cikin shekaru uku da suka gabata.
A binciken da kafar yaɗa labarai ta BBC ta yi bisa bayanai daga cibiyar SBM Intelligence kamfani da ke tattara bayanan tsaro a nahiyar Afirka – hare-haren da ake danganta wa Boko Haram sun ƙaru daga 105 a shekarar 2022, zuwa 147 a sekarar 2023, sannan suka kai 191 a shekarar 2024.
A shekarar 2025 kuma, harin farko da Boko Haram ɗin suka kai ya faru ne a ranar 4 ga watan Janairu, lokacin da Boko Haram ta yi wa sojojin Najeriya kwanton ɓauna a kauyen Sabon Gari, inda suka kashe sojoji shida. Kwana tara bayan haka, a ranar 13 ga Janairu, ƙungiyar ta sake kai wani hari a ƙauyen Dumba kusa da Baga, inda ta kashe manoma da masunta 40.
Tun daga wannan lokaci, ƙungiyar Boko Haram ta ci gaba da kai hare-hare a kowane wata a wannan shekara, tare da ƙaruwar yawan su. Wannan yana nuna wata matsala ta sake dawowar tashin hankali, musamman a yankunan karkara da kuma gefen birane.
ranar 8 ga watan Afrilun 2025, gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa game da dawowar hare-haren Boko Haram da kuma ƙaruwar sace-sacen mutane. Ya ce ƙungiyar na ƙoƙarin dawowa inda sau da dama ta kai hari kan sansanonin sojoji da kashe fararen hula.
“Kashe fararen hula da jami’an tsaro abin damuwa ne matuka, kuma yana nuna koma baya mai girma ga jihar Borno da yankin arewa maso gabas gaba ɗaya,” in ji Zulum.
Rahotanni daga jihohin Borno da Yobe na nuna cewa ƙaruwar hare-haren ƙungiyar na nuni da cewa ba a ci galaba ba yadda ake tunani wajen kawar da ƙungiyar.
“Abin da muka gani ba ƙaramin abu bane, yana nuna cewa mutane na fara rasa fata da karfin gwiwa. Kowa na cikin tsoro, zuciya cike da fargaba, mutane na kokarin daidaita tunaninsu,” in ji Aliyu Harande, wani mazaunin garin Mafa, cikin hirarsa da BBC bayan harin da aka kai a shekarar da ta gabata.
“Ga mu da muka ɗauka cewa hare-haren Boko Haram ɗin sun lafa, wannan harin ya bayyana mana cewa ba haka bane, harin ya nuna mana cewa suna sake taruwa” in ji shi.
Zanna Umara, wani jami’i a ƙaramar hukumar Tarmuwa, ya shaida wa BBC cewa: “Ba ma fatan dawowarsu, amma ganin irin harin da suka kai a Mafa, yana nuna kamar da gaske suna kokarin dawowa ne.”
Dr. Kabir Adamu, shugaban kamfanin tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited kuma masani a fannin tsaro ya ce ƙaruwar hare-haren da ake gani a baya-bayan nan na da nasaba da wasu dalilai.
Na farko, in ji shi, shi ne sakin wani umarni daga kungiyar ISIS da ke buƙatar duka rassanta su kara yawan hare-hare, kuma an ga ƙungiyoyi daban-daban suna amsa wannan kiran.
Abu na biyu da Dr. Adamu ya danganta karuwar hare-haren Boko haram da shi shi ne wani yanayi na lokaci.
“Kafin lokacin damina, wadannan ƙungiyoyi sukan ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare, domin sun san ayyukan soji kan ragu a lokacin saboda wahalar hanya da ƙarancin gani,” in ji shi.
Ya kara da bayyana cewa rashin zaman lafiya a yankin Sahel na daya daga cikin manyan dalilai. “Tashe-tashen hankula a Sahel, musamman a kasashen Chadi da Nijar da Burkina Faso, sun raunana tsaron iyakoki, hakan ya bai wa waɗannan ƙungiyoyi damar motsawa da ɗaukar sabbin mambobi da samun tallafi cikin sauki,” in ji masanin.
Dr. Adamu ya kuma ce sauye-sauyen da aka yi a tsarin rundunar sojin Najeriya sun taimaka wa Boko Haram ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare musamman yadda aka mayar da kayan yaƙi da sojoji daga arewa maso gabas zuwa arewa maso yamma domin sabbin hare-hare.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce karuwar hare-haren Boko Haram yana da nasaba da yawaitar ayyukan ‘yan tada ƙayar baya a ƙasashen makwabta.










