• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yadda Ƙasar Birtaniya ta fitar da sabbin dokokin magance shigar Baƙin haure ƙasar

aksam by aksam
May 12, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya zayyana wasu matakai da za a bi domin tsaurara dokokin shiga da zama a ƙasar, da zimmar rage kwarorowar baƙi masu zuwa zama da karatu da neman aiki.

Daga cikin matakan akwai gwajin Ingilishi ga dukkan masu neman izini shiga ƙasar da kuma tsawaita lokacin da ake ɗauka a ƙasar kafin samun izinin zama na dindindin.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Firaministan yana kuma so a rage ɗaukar ma’aikatan jinya daga ƙasashen ƙetare, matakin da zai taimaaka wajen rage yawan ƴan ƙsashen waje da ake ɗauki aiki a ƙasar ta sahihiyar hanya.

Sai dai bai ce komai ba game da masu shiga ƙasar ta ɓarauniyar hanya, kamar masu shiga ta teku.

Adadin baƙin da suka shiga ƙasar a shekarar 2024 sun kai 728,000 zuwa watan Yunin shekarar.

Hukumomin ƙasar za su fitar da gamsasshen bayani mai ɗauke da sababbin tsauraran matakan, waɗanda za su ƙunshi na mallakar izinin karatu da aiki a Birtaniya.

Sakataren harkokin baƙi na Birtaniya Yvette Cooper ta bayyana wa BBC cewa lokaci ya yi da za su rage ɗaukar ma’aikatan jinya daga ƙasashen waje.

Ta ce wannan matakin zai taimaka wajen rage kusan mutum 50,000 waɗanda ba ƙwararru ba ne sosai da suke shiga ƙasar daga ƙasashen ƙetare a duk shekara.

Firaministan ya ce sababbin matakan za su taimaka wajen “sake mallake bakin iyakokin ƙasarmu.”

Idan aka ɗabba sabbin matakan nan da gwamnatin ƙasar za ta ɗauka, ƴan ƙasashenmutane daga ƙasashen Najeriya da Pakistan da Sri Lanka za su fuskanci ƙalubale wajen samun izinin shiga ƙasar Birtaniya domin karatu.

Starmer ya ce Birtaniya za ta riƙa neman waɗanda suka fi ƙwarewa ne a duniya wajen ɗaukar aiki, sannan za su bincika me ya sa wani ɓangaren aikin ƙasar ya fi mayar da hanakali kan “neman sauƙi wajen ɗaukar aiki.”

Firaministan ya ce sabbin matakan za su fayyace komai da komai game da tsare-tsaren shige da fice a ƙasar – iyali da karatu da aiki.

“Zan tabbatar da matakan nan saboda za su tabbatar da adalci, kuma abin da ya dace ke nan,” in ji Starmer a wani taron manema labarai.

Ya ce bai kamata a riƙa mayar da hankali kan neman sauƙi wajen ɗaukar ma’aikata ba, maimakon mayar da hankali kan horar da matasan ƙasar.

Starmer ya ƙara da cewa baƙin da suke shigowa ƙasar a gwamnatin baya sun kai kusan miliyan 1 a shekarar 2023, wanda shi ne adadi mafi yawa.

Ya ce adadin baƙin ya kai adadin mutanen birnin Birmingham baki ɗaya, wanda kuma shi ne birni na biyu mafi girma a Birtaniya.

“Wannan ba ci gaba ba ne, kasada ce. Ba zai yiwu a ce da kuskure hakan ya faru ba, wannan ganganci aka yi

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Bukola Saraki Zai Jagoranci Sulhunta ‘Ya ’Yan Jam’iyyar PDP

Next Post

Wani Dan Majalisar Jihar Kano Ya Sauya Sheka Daga NNPP Zuwa APC

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Saukar karatun Al’qur’ani Dari 600

April 8, 2024
Shugaban Jam’iyar APC Na Kasa; Sun Hadu Da Sanata Kawo Sumaila

Shugaban Jam’iyar APC Na Kasa; Sun Hadu Da Sanata Kawo Sumaila

December 20, 2023
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media