Ƙungiyar kwadago ta Trade Union Congress of Nigeria (TUC) ta bai wa gwamnatin tarayya shawarar hanyar da zata magance ƙarancin abinci cikin mako biyu.
Kamar yadda Punch ta tattaro, TUC ta buƙaci gwamnatin tarayya ta fara shigo da kayayyakin abinci domin rage
Shugaban kungiyar ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana hakan a taron manema labarai kan matsin tattalin arzikin da kasar nan ke ciki a birnin tarayya Abuja.
A cewarsa, ‘yan Najeriya ba su taba shiga irin wannan wahalhalun na tsadar rayuwa ba ko a lokacin mulkin soja.
Ya ƙara da cewa waɗannan matsalolin sun samo asali ne daga rashin maida hankalin gwamnati wajen samar da kaya a cikin gida da kuma ba su fifiko.
Shugaban TUC ya ce: “Ƴan Najeriya na buƙatar su ji su a ƙoshe ta yadda zasu iya fahimtar kyaun tsarukan da gwamnati ta ɓullo da su. Ya kamata a sassauta kokarim wadatar abinci a cikin gida.
Ya kamata gwamnatoci na kowane mataki su gaggauta zuwa su siyo isassun kayan abinci daga sassa daban-daban na duniya tare da raba wa ga ƴan Najeriya marasa galihu.












