Har yanzu ‘yan Najeriya na cikin rudani duk da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabi a ranar Alhamis kan ci gaba da aiwatar da kudurin daina amfani da tsaffin takardun kudi a Najeriya tare da bada tabbacin cewa gwamnati na yi duk mai yiyuwa wajen samar da wadatattun sabbin takardun kudi.
Shugaban kasa ya kara da cewa za a hukunta duk wanda aka samu da laifin yiwa tsarin sabbin takardun kudin zagon kasa. Sai dai masu hada-hadar POS na ci gaba da cin karensu babu babbaka ganin yadda suke tsawallawa ‘yan kasa wajen cajar kudin da ake biya idan za’a cira kowanne dubu 1 a kasar, lamarin da ke kara jefa mutane cikin mawuyacin hali.
Wannan al’amari na janye tsaffin takardun kudin naira 200, 500 da 1000 daga amfani ga ‘yan kasa na ranar 10 ga watan Febrairu kafin shugaba Buhari ya sanar da dawo da amfani da naira 200 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu na ci gaba da jawo rudani musamman ma ganin yadda rahotanni daga sassan Najeriya daban-daban suka yi ta nuni da cewa wasu gwamnonin arewa sun yi biris da jawabin da shugaba Buhari ya gabatar a ranar Alhamis suna masu umartar mazauna jihohinsu da su ci gaba da yin amfani da tsoffin takardun kudin wajen gudanar da ayyukan su na yau da kullum.












