Afrika ta Kudu – Wani mutum da ya yi iƙirarin cewa shi ma’aiki ne, ya nutse cikin ruwa kuma nan take kada suka yi kaca-kaca da naman shi a lokacin da ake yin baftisma.
A ranar Lahadi ne aka fara gano sauran sassan jikin mutumin zagaye da kadoji a rafin Olifants da ke Limpopo, na Afrika ta Kudu suka yi hafzi da shi, kamar yadda jaridar MailOnline ta ruwaito.
Mutumin mai shekaru 48 wanda ya yi ikirarin shi ma’aiki ne ya fito daga yankin Atok, kuma ya nutse a rafin ne yayin da ya ke yin baftisma da wasu mutum biyu.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na yankin, Kanal Malesela Ledwaba, ya sanar da cewa:
“Ana zargin cewa kadojin ne suka farmake shi yayin da ya ke baftisma.
” Yan sanda sun ce daya daga cikin malaman cocin da suka je rafin sun yi kokarin nemo dan uwan nasu da ya nutse amma abin ya ci tura.












