Babban limamin cocin evangelical, Primate Elijah Ayodele ya ce tilas ƴan adawa su haɗa maja idan suna son kayar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Primate Ayodele ya buƙaci ƴan adawa su ajiye banbanci, su haɗe kai wuri ɗaya sannan su tsayar da ɗan takara ɗaya tilo da zai gwabza a zaɓen shugaban ƙasa na gaba.
Malamin addinin kiristan ya yi wannan furucin ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa kwanan nan a shafinsa na X watau Twitter
A baya Ayodele ya gargaɗi jam’iyyar PDP da kar ta sake ta yi kuskuren baiwa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar takara.
Faston ya ce idan PDP ta sake ba Atiku takara a 2027, to ta zama gawa domin ba za ta kai labari ba. Malamin ya faɗi hanyar kifar da Tinubi
A wannan karon kuma fitaccen limamin ya ce dole sai ƴan adawa sun dunƙule wuri ɗaya sannan za su iya turmushe Shugaba Tinubu a akwatun zaɓe.
“Idan kuna son kayar da Tinubu dole sai kun haɗa kai. Haɗuwar ku wuri ɗaya ne kaɗai zai iya kawo ƙarshen mulkin APC a zaɓen 2027











