Majalisar Ɗinkin Duniya da Netherlands sun soke taron masu auren jinsi a Senegal bayan kakkausar gargaɗin gwamnatin ƙasar ta
Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙasar Netherlands sun yi gaggay soke wani taron da su ka shirya gudanarwa na kare haƙƙin masu auren jinsi (LGBTQ) a birnin Dakar na Senegal, bayan da gwamnatin ƙasar ta nuna ɓacin ranta tare da adawa da shi.
Taron wanda ofishin kare haƙƙin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin kasar Holland suka shirya domin inganta tattaunawa kan haƙƙin ƴan LGBTQ, an shirya gudanar da shi ne a ofishin jakadancin ƙasar Holland da ke Dakar.
Sai dai gwamnatin Senegal ta fitar da wata sanarwa mai kakkausar gargaɗi, ta na mai cewa irin wannan lamari ya saɓa wa al’adu da addinin ƙasar tare da ƙara yin gargaɗin cewa ba a amince da irin wadannan ayyuka ko nau’ikan fafutuka a ƙasar ba.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa ƙasashen yammacin Afirka ciki har da Senegal na da dokar haramta harkokin masu auren jinsi, inda aka tanadar da hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan yari ga duk wanda aka same shi da laifi makamancin wannan.












