Daga Hassan Umar Gwammaja
Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara dake Najeriya ta buƙaci a gaggauta gudanar da bincike domin gano dalilin da ya sa sojoji suka harbe DPO’n Wasagu, Halliru Liman, a kan hanyarsa ta tafiya Birnin Kebbi, domin halartar taron wata-wata.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Yazid Abubakar, ya ce sojoji sun harbe Liman ne a kan hanyar Ɗanmarke da ke ƙaramar hukumar Maru, inda sojojin da ke aiki a rundunar Hadarin Daji suke duba ababan hawa.
Kakakin ya ce duk da gabatar da kansa garesu, jami’an sojin sun ƙi saurarensa inda suka harbe shi har lahira.
Wannan kisa dai ya daɗa fitowa da ɓarakar da ke tsakanin ɓangarorin tsaron Najeriya na rashin aiki tare.
Tuni dai ƴan Najeriya suka fara Allah wadai da kisan gillar.












