Mutane fiye da dubu 15 a kananan hukumomi 22 na Jihar Kano sun amfana da shirin duba lafiyar baki da hakora da ba da magani kyauta a karkashin shirin kula da lafiyar baki da gwamnatin jihar take daukar nauyi.
Babban jami’i Mai Kula da Lafiyar Baki na Hukumar Kula da Lafiyar Farko ta Jihar Kano, ‘Therapist’ Nura Aliyu Sa’id, ne ya bayyana hakan a cikin shirin Radio Kano mai suna _’Yau da Gobe’.
Ya ce ayarin likitocin hakori na zagayawa zuwa garuruwa domin duba lafiyar hakora kyauta, musamman a yankunan karkara da ba su da asibitocin hakori.
Nura Aliyu Sa’id, ya ce, kashi 80 cikin 100 na jama’a na fama da matsalar hakora , kuma shirin ya taimaka wajen gano cututtukan baki da suka dade suna boye a cikin yara, ciki har da wadanda suke yaduwa daga uwa zuwa jaririnta.
Ya kara da cewa, zamani ya wuce na cire hakori domin yanzu masana na da hanyoyin magance kowace irin matsalar hakori.
A nasa jawabin, Mataimakin shugaban shirin Mai Kula da shiyyar Rano, ‘Therapist’ Kabiru Ibrahim Dawakin Kudu, ya ce lalacewar hakori da sauran cututtukan baki na faruwa ne a saboda rashin tsafta da rashin wanke baki akai-akai.
Ya bukaci jama’a su rika wanke baki akai-akai, tare da neman shawarar kwarru akan man goge baki da burushin da ya dace da su.
Masana sun jaddada bukatar jama’a su rika zuwa asibiti domin duba hakoransu aƙalla sau biyu a shekara domin dubawa, da kuma neman magani da zarar sun ga canji a hakoransu.
Daga bisani, sun yaba da kokarin Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa daukar nauyin shirin, tare da jinjinawa sauran shugabanni da jama’a masu kishin al’umma da ke tallafawa wajen magance matsalolin lafiyar baki a jihar Kano.










