Kotu a kasar Saudiyya ta yanke hukuncin ɗaurin shekara 20 ga tsohon shugaban harkokin tsaron ƙasar kan laifukan Rashawa.
Daily Nigeria Hausa ta rawaito cewa kotun ta ci tarar Janar Khalid Bin Qarar al-Harbi, dala 250,000 tare da umartarsa ya maido da kuɗaɗen da suka kai dala miliyan 3.5 na rashawa da ya wawushe.
An samu tsohon jami’in – da ya riƙe wannan muƙami a ma’aikatar tsaro na tsawon shekara shida – da laifukan zamba da karɓar kuɗaɗen toshiya da amfani da muƙaminsa wajen biyan buƙatun kansa.
Hukuncin shi ne na ƙarshe kuma babu damar daukaka kara. Ma’aikatar cikin gida ta ƙasar ta jaddada ƙudurin gwamnatin ƙasar na ci gaba da yaƙi da duk wani nau’in cin hanci da rashawa.









