• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Jamhuriyar Nijar Na Son Ƙara Adadin Jihohinta Daga 8 Zuwa 19 Da Kuma Sauya Sunayen Wasu Jihohin

aksam by aksam
May 14, 2026
Reading Time: 2 mins read
0
Home KETARE
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Hassan Umar Gwammaja

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da Tsaro ta Nijar ta gabatar da wani sabon daftarin dokar sake fasalin rabon yankunan ƙasar, wanda zai ƙara adadin jihohin Nijar daga takwas zuwa 19.

RelatedPosts

Yayin Da Wa’adin Da Shugaban Trump Ya Baiwa Iran Na Sake Bude Mashigin Hormuz Ke Gabatowa, Rahotannin Sun ce Magoya Bayan Gwamnatin Iran Sun Fantsama Kan Tituna Tare Da Yin Tattaki A Wasu Tashoshin Wutar Lantarki

A Yayin Da Babbar Sallah Ke Kara ƙaratowa, ’Yan Kasuwar Dabbobi Sun Bayyana Fargaba Game Da Yiwuwar Farashin Ragunan Layya Da Sauran Dabbobi Zai Yi Tashi Gwauron A Najeriya

Kasar Nijar Ta Dakatar Da Fitar Da Dabbobi Zuwa Ƙetare Gabanin Sallah

Kamfanin dillancin labaran ƙasar, ANP ya ruwaito cewa shirin ya kuma tanadi ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 20 domin ƙarfafa kasancewar gwamnati a faɗin ƙasar da kuma inganta shugabanci a matakin ƙananan hukumomi.

A cewar gwamnatin ƙasar, sabon tsarin zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da walwalar jama’a, tare da inganta ayyukan tsaro da gudanar da harkokin gwamnati bisa la’akari da ƙalubalen tsaro da ci gaban al’umma.

Wannan sauyi na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin mulkin sojin Nijar ke ci gaba da aiwatar da sauye-sauye a tsarin mulki da gudanarwar ƙasar tun bayan hambarar da gwamnatin farar hula a watan Yulin 2023.

Bisa ga sabon tsarin, jihohin Agadez da Diffa da Dosso za su samar da jihohi biyu-biyu, yayin da jihohin Maradi da Tahoua da Tillabéri da Zinder kowacce za ta samar da jihohi uku. Sai dai Yamai ce kaɗai za ta ci gaba da kasancewa jiha guda ɗaya.

Baya ga ƙirƙirar sabbin jihohi, gwamnatin Nijar ta kuma sauya sunayen tsoffin jihohi takwas na ƙasar.

A ƙarƙashin sabon tsarin:

• Diffa za ta koma Komadougou

• Zinder za ta koma Damagaram

• Maradi za ta koma Katsina

• Dosso za ta koma Ziggui

• Tillabéri za ta koma Issa

• Agadez za ta koma Abzine

• Tahoua za ta koma Ader

Sai dai Yamai ce kaɗai za ta ci gaba da amfani da tsohon sunanta.

Sauran sabbin jihohin da za a ƙirƙira sun haɗa da Kawar da Mangari da Arewa da Tazar da Gobir da Azawak da Magia da Tougana da Kourfey da Daoura da Damergou.

Wasu daga cikin sababbin sunayen jihohin sun samo asali ne daga tsoffin masarautu da yankunan tarihi da suka yi fice a Nijar tun kafin mulkin mallaka.

Haka kuma, daftarin dokar ya tanadi ƙirƙirar sabbin manyan biranen jihohi 15 da kuma sabbin ƙananan hukumomi 20, ciki har da Tabelot da Djado da Chétimari da Dogon Kiria da Guéchémé da Sambéra da Tibiri da Ourafane da Kornaka da Kanambakaché da Hamdallaye da Bambèye da Kaou da Ourno da Tamaské da Goroual da Makalondi da Kellé da Gangara da Guidimouni.

Rahoton ya ce sabbin ƙananan hukumomin za su rabu tsakanin jihohin ƙasar daban-daban, inda Maradi da Tahoua za su samu huɗu-huɗu, Dosso da Zinder uku-uku, Agadez da Tillabéri biyu-biyu, yayin da Diffa da Yamai za su samu guda ɗaya kowacce.

Advertisement
Wannan sauyi na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin mulkin sojin Nijar ke ci gaba da aiwatar da sauye-sauye a tsarin mulki da gudanarwar ƙasar tun bayan hambarar da gwamnatin farar hula a watan Yulin 2023.

Nijar dai na fama da hare-haren ‘yanta’adda musamman a yankunan Tillabéri da Diffa da Tahoua, lamarin da hukumomi ke cewa sabon tsarin gudanarwa zai taimaka wajen ƙara kusantar gwamnati da jami’an tsaro zuwa yankunan karkara.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Ƙungiyoyi 25 Sun Nemi Bincike Kan Shigar CAGSI Cikin Shirin GAVI a Kano

Next Post

An Kama Wata Matashiya Mai Shekaru 27 Bisa Zargin Satar Jariri A Asibiti A Zamfara

aksam

aksam

RelatedPosts

Yayin Da Wa’adin Da Shugaban Trump Ya Baiwa Iran Na Sake Bude Mashigin Hormuz Ke Gabatowa, Rahotannin Sun ce Magoya Bayan Gwamnatin Iran Sun Fantsama Kan Tituna Tare Da Yin Tattaki A Wasu Tashoshin Wutar Lantarki
KETARE

by aksam
April 7, 2026
Kasar Nijar Ta Dakatar Da Fitar Da Dabbobi Zuwa Ƙetare Gabanin Sallah
KETARE

A Yayin Da Babbar Sallah Ke Kara ƙaratowa, ’Yan Kasuwar Dabbobi Sun Bayyana Fargaba Game Da Yiwuwar Farashin Ragunan Layya Da Sauran Dabbobi Zai Yi Tashi Gwauron A Najeriya

by aksam
May 18, 2025
Kasar Nijar Ta Dakatar Da Fitar Da Dabbobi Zuwa Ƙetare Gabanin Sallah
KETARE

Kasar Nijar Ta Dakatar Da Fitar Da Dabbobi Zuwa Ƙetare Gabanin Sallah

by aksam
May 11, 2025
Rashawa: Kotun Saudiyya ta yanke ɗaurin shekara 20 ga tsohon babban hafsan tsaron kasar
KETARE

Rashawa: Kotun Saudiyya ta yanke ɗaurin shekara 20 ga tsohon babban hafsan tsaron kasar

by aksam
September 15, 2024

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

DPO, Mutane biyu sun rasa ransu yan awanni Kafin Daura masa Aure

DPO, Mutane biyu sun rasa ransu yan awanni Kafin Daura masa Aure

June 16, 2025
Babbar Kotun Tarayya Dake Zamanta Abuja; Karƙashin Mai Shariʼa Peter Odo Lifu  Ta Bayar Da Umarnin A Sakin Sheikh Sani Khalifa Zaria Ba Tare Da Bata Lokaci Ba

Babbar Kotun Tarayya Dake Zamanta Abuja; Karƙashin Mai Shariʼa Peter Odo Lifu Ta Bayar Da Umarnin A Sakin Sheikh Sani Khalifa Zaria Ba Tare Da Bata Lokaci Ba

April 20, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Hukumar Tace Fina-finai Ta Kano Ta Dakatar Da Wasu Jaruman Kannywood Biyu

Hukumar Tace Fina-finai Ta Kano Ta Dakatar Da Wasu Jaruman Kannywood Biyu

May 17, 2026
Yadda Wata Mata Ta Banka Wa Mijinta Da Amaryarsa Da ‘Ya’yanta Guda Biyu Wuta A Kano ‎ ‎

Yadda Wata Mata Ta Banka Wa Mijinta Da Amaryarsa Da ‘Ya’yanta Guda Biyu Wuta A Kano ‎ ‎

May 13, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media