Tun bayan da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya faɗi cewa “zamanin tallafi ya wuce” a jawabinsa na kama aiki a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ƴan Najeriya suka tsinci kansu a wani sabon babin rayuwa da wataƙila ba su taɓa tsammani ba.
“Mun yaba wa shawarar gwamnatin da ta gabace mu na cire tallafin man fetir wanda yake amfanar masu arziƙi fiye da talakawa. Ba za a iya ci gaba da biyan kuɗi tsubububa a matsayin tallafi a daidai lokacin da lalitar gwamnati ke ci gaba da tsiyayewa. Za mu karkatar da kuɗaɗen zuwa wasu hanyoyin mafiya amfani kamar gine-ginen gwamnati da Ilimi da fannin lafiya da kuma samar da ayyukan yi domin inganta rayuwar miliyoyin ƴan ƙasar.” In ji Shugaba Bola Tinubu, a jawabin nasa na kama aiki ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Bisa jawabin na Tinubu, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ce ta cire tallafin inda shi kuma ya yi sanarwa.
Jim kaɗan bayan jawabin nasa sai aka fara samun dogayen layukan mai a manyan biranen ƙasar kamar Legas da Abuja da Kano.









