Bayan ya shafe shekara 20 a Majalisa, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Ahmed Mirwa Lawan, ya sha kaye a hannun matashi mai shekara 35.
Lawan, na jam’iyyar APC dai ya sha kayen ne a hannun Lawan Musa na jam’iyyar PDP a mazabar Nguru II.
Wannan shi ne karo na biyu suke fafatawa da kakakin majalisar sai a wannan karon ne ya samu nasarar lashe zaben.
Kamar yadda jami’in tara sakamakon zaben wannan mazaba ta wajen Nguru Dr Habib Muhammad ya bayyana cewar, Dan takarar Jam’iyyar ta PDP Musa Lawan ya kada kakakin majalisar Hon Ahmad Lawan Mirwa, ne da Kuri’u, 6,648 yayin da shi kakakin majalisar dokokin ya samu Kuri’u 6,466.
Wata majiya da ke garin na Nguru ta bayyana cewar, an so a samu ‘yar hatsaniya a wannan mazaba ta wajen Nguru sakamakon kokarin yin jinkiri shelanta wanda ya ci zaben sai da matasa suka yi barazanar kunna wuta a ofishin tattara sakamakon zaben wadda ganin cewar jinkirta shelanta wanda ya ci zaben kan iya haifar da matsala.









