Kungiyar matuka motocin Akorikura ta Kasa reshen jihar Kano, ta Shawarci Gwamnatin jihar Kano da ta Nemawa masu Akorikura da sauran masu gudanar da harkokin Sufuri matsuguni a Sabuwar Kasuwar Dangwauro da aka bude anan jihar Kano.
Sakataren Kungiyar Alh. Naziru Sani Dandago ne ya ba da Shawarar a Lokacin da yake Zantawa da manema labarai a ofishin Kungiyar dake Hanyar Murtala Mohammed a nan Kano.
Naziru Dandago ya bayyana cewa, Idon Gwamnati ta samarwa ‘Ya’yan Kungiyar Akorikura ta (NURTW) gurin tsayawa na din_din _din,zai baiwa Gwamnatin samun Kudaden Haraji da samarwa matasa Ayyukan yi da za su rage masu Zaman kashe Wando a lungu da sako na jihar Kano.
Sakataren yace, Gwamnatin Kano tana barin Kudade da dama suna zirarewa,Wanda ita ce ya kamata tana karba daga hannun Direbobin da suke Sufuri a jihar Kano da kuma, makwabtan jihohi.
Yace, Kungiyoyin harkokin Sufuri a shirye suke wajen ganin sun baiwa Gwamnatin cikakken hadin kai da goyan baya domin Raya Kasuwar Dangwauro da yankunanta.
Naziru Sani ya bayyana cewa, Kungiyar ‘yan Akorikura ta Dade tana Neman Gwamnati ta samar mata guraren tsayawa sai kuma gashi wannan Kasuwa ta Dangwauro ta bayyana a dai dai lokacin da ake bukatarta.
Ya kara da cewa,idon Gwamnatin Kano tana bukatar bunkasa harkokin Sufuri da Kasuwar ta Dangwauro, to ya kamata ta baiwa Kungiyar Direbobin Akorikura wuri a kasuwar, saboda gudunmawar da matuka motoci suke bayarwa a ciki da wajen jihar Kano.
Ya bayyana cewa, Gwamnatin Kano tana kokarin cika Alkawari da zarar ta ayyana za ta gabatar da wani al’amari domin inganta rayuwar matasa da alummar jihar Kano.
Sakataren ya jaddada goyan bayan da suka kamata ga Gwamnati da sauran Hukumomin da suke lura da harkokin Sufuri ta yadda za’a Nasara na tattara kudaden harajin da Gwamnati za ta aiwatar da managartan ayyukan ci gaba da sauran abubuwan da za su bunkasa jihar Kano.
Kungiyar ‘yan Akorikura ta kuma shawarci sauran Kungiyoyin Sufuri, da su hada kai wuri guda domin ciyar da harkokin Sufuri gaba domin yin gogayya da sauran Kungiyoyi dake makwabtan jihohi, Kasacewar suna samun tagomashi daga Gwamnatoci na jiha da na tarayya,Musamman wajen basu tallafi da motocin da Kungiyoyin Sufuri za su rabawa ‘Ya’yanta domin su samu damar mallakar ta su.
Daga karshe Naziru Sani Dandago, ya bukaci ‘yankungiyar Akorikura ta kasa reshen jihar Kano, da su kara kaimi wajan baiwa Gwamnati da Kungiyar Direbobin cikakken hadin kan da ya dace,domin cimma burin da aka sanya a gaba.










