• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kalli mataki na biyu na mayar da fadar mulkin Nageriya Legas

Sy lawan by Sy lawan
January 27, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Haramta amfani da kwalaben roba a Jihar Legas cibiyar kasuwanci a Nijeriya ya janyo mayar da martani daga bangarori daban-daban.
Gwamnatin jihar Lagos ta bayyana cewa an hana amfani da kwalaben robar ne don kubutar da muhalli daga gurbacewa. Hoto: Reuters

Gwamnatin Jihar Legas a Nijeriya, yanki mai dimbin jama’a, na fama da datti da bola da ke addabar mazaunan jihar tare da gurbata muhalli. Babbar sharar da ta fi damun jihar ita ce kwalaben roba da ake zubarw aa kan tituna da cikin teku.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

A baya-bayan nan gwamnatin ta sanar da haramta amfani da kwalaben roba da kwanon soyoyo na zuba abinci, a matsayin wani bangare na matakan magance matsalar da ta munana tsawon shekaru.

Wasu na bayyana cewa wannan mataki bai zo rana guda ba. Wasu kuma na kira da a samar da mafita kafin aiwatar da wannan haramci.

A matsayin ta na jiha mafi cunkoson jama’a a Nijeriya, Legas ta shirya rayuwa ba tare da kwalaben roba da mazubin abincin soyoyo ba, an samu rarrabuwar ra’ayin jama’a kan haramta samarwa da sayar da wadannan abubuwa biyu.

Ga jihar da samun tarin sharar kwalaben roba har tan 870,000 a shekara, watakila matakin farko na haramci, saboda yadda yawaitar jama’a kan iya sanya abubuwa su fi karfin yadda za a magance su.

Da yake sanar da haramcin ta shafinsa na X, kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa na Jihar Legas, Tokumbo Wahab ya shaida cewa an dauki matakin ne saboda matsalar gurbata muhalli da robobi ke yi.

Wannan mataki na haramci na farko a Nijeriya ya janyo mayar da martani daban-daban.

“Haramcin kwalaben roba da mazubin abinci na soyoyo ya yi daidai da kokarin da duniya ke yi na yaki da gurbata muhalli da roba ke yi, da kuma tabbatar da kyakkaywan muhalli mai dore wa,” in ji Alex Akhibe, wanda ya samar da wata kungiya ta kare muhalli mai sunan, African Cleanup Initiative yayin da yake tataunawa da manema labarai.

Ya ce “Hakan na nuni da kokarin magance matsalolin muhalli da kuma karfafa gwiwar amfani da wasu abubuwan da suka fi alfanu ga muhalli. Wannan cigaba ne mai kyau da z aa amince da shi.”

Amma ba kowa ne ya amince da Alex ba game da wannan haramci. A yayin da wasu ke ganin tuntuni ya kamata a ce an aiwatar da hakan, wasu kuma ba su da tabbacin ko mahukunta sun yi daidai wajen saka haramcin, kafin a ce an samar da wasu kayan da za su maye gurbin robobin.

Tsaunin shara

Abun da babu mai gardama a kai shi ne hada-hada da ake samu a garin na gabar teku da ya zama babban birnin kasuwancin kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka. Jihar Legas na da fadin kasa mai girman sukwayamita 3,577, ind atake dauke da kusan mutane miliyan 21.

Yawan jama’a na ci gaba da daduwa, a yayin da kowa ke kokarin amfana da hada-hadar da ake yi a garin.

Duk da cewa Legas na da wajen ajje shara kamar su Olusosun da Epe, wannan bai wadatar ba.

Tare da yawiatar jama’a, jihar na bukatar karin sarari don samar da gidaje, wanda wannan ma wani kalubale ne na samar da karin wuraren tara shara musamman kwalaben roba da mazubin abinci na soyoyo.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Mutane 154′ sun kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane

Next Post

A ci gaba da kula kawance da kasashen Africa Putin ya bayar da Alkama tan 25,000 ga kasar Burkina Faso

Sy lawan

Sy lawan

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Kasafin kudin 2025/2026, Tinubu zai ciyo bashin Dala biliyon 21 da fam biliyon 4 da yon biliyon 15

Kasafin kudin 2025/2026, Tinubu zai ciyo bashin Dala biliyon 21 da fam biliyon 4 da yon biliyon 15

July 23, 2025
Yadda Hukumar kashe Gobara ta kubutar da Mutane biyu daga Rijiya a Mabanbanta gurare

Yadda Hukumar kashe Gobara ta kubutar da Mutane biyu daga Rijiya a Mabanbanta gurare

June 30, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media