Daga Hassan Umar Gwammaja
An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga Disamba, 1942 a Daura, Jihar Katsina. Ya shiga soji a shekarar 1961, sannan daga baya ya zama shugaban kasa na mulkin soja daga 1983 zuwa 1985.
Daga baya kuma ya sake dawowa mulki a matsayin zababben shugaban kasa daga shekarar 2015 zuwa 2023 bayan nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen shugaban ƙasa.
Tsohon shugaban ya kasance mutum mai matuƙar tsari da gaskiya, wanda ya kafa tarihi a yakin da ya yi da cin hanci da rashawa da kuma gyaran tattalin arziki.
Tuni shugaban ƙasa da na kasashen waje, shugabannin addinai, ‘yan siyasa da dubban ‘yan Najeriya suka fara aikawa da saƙonnin ta’aziyya da addu’o’i ga iyalansa da al’ummar kasar.
Majalisar Ministoci ta ayyana kwanaki uku na zaman makoki tare da daga tutocin ƙasa rabin sanda a duk faɗin Najeriya.











