RelatedPosts
Jam’iyyar ta ce an tsara katin ne da nufin ɓata mata suna tare da jefa ta cikin rikicin siyasa da na tsaro, musamman a yankin Arewa maso Yamma.
A cewar kakakin jam’iyyar APC, jam’iyyar ba ta taɓa yi wa Bello Turji rajista a matsayin ɗan jam’iyya ba, kuma ba za ta taɓa amincewa da shigar duk wani mutum da ke da alaƙa da ta’addanci ko ‘yan bindiga cikin jam’iyyar ba.
APC ta kuma bayyana cewa tana haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin gano mutanen da ke da hannu wajen ƙirƙira da yaɗa katin, tare da ɗaukar matakan shari’a a kansu.
Jam’iyyar ta yi kira ga al’umma da su yi watsi da katin, tana mai jaddada matsayinta na goyon bayan yaƙi da ‘yan bindiga da ta’addanci a Jihar Zamfara da sauran sassan Arewa maso Yamma.
APC ta ƙara da cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare mutuncinta da kuma tallafa wa duk wani ƙoƙari na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya.











