• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Hedikwatar Tsaro Ta Ƙasa Ta Tabbatar Da Kama Wasu Jami’an Tsaro Huɗu Da Ake Zargi Da Taimakawa Ayyukan Ta’addanci A Yankin Arewa Maso Gabas

aksam by aksam
May 4, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home TSARO
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana neman jami’inta ruwa a jallo

Peace Corps of Nigeria Ta Yi Bikin Cika Shekaru 28 da Kafuwa

Jerin kamfanin tsaro na Amurka 10 da ‎China Ta Kakaba wa Takunkumi

Daga Hassan Umar Gwammaja

Bayanan da Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ya fitar, an cafke jami’an ne a yayin wani samame da dakarun tsaro suka gudanar daga ranar 26 zuwa 29 ga Afrilu, 2025 a ƙananan hukumomin Bama, Kukawa, da Madagali dake Jihohin Borno da Adamawa.

Manjo Janar Kangye ya bayyana cewa, biyu daga cikin jami’an da aka kama na daga cikin rundunar haɗin gwiwa da ke aiki tare da sojojin ƙasar wajen yaƙi da ta’addanci.

“A cikin waɗanda muka kama akwai jami’an tsaro da ke bai wa ’yan ta’adda bayanai da kayan aiki. Wannan lamari abin takaici ne kuma ya nuna irin cin amanar da ke faruwa a cikin rundunar,” in ji Kakakin

Ya ƙara da cewa, rundunar sojoji ta kama wasu ’yan ta’adda huɗu da ke da alaƙa da waɗannan jami’ai, kuma an tabbatar da cewa suna taimaka wa masu kai farmaki da kayayyakin yaƙi da bayanan sirri.

Manjo Janar Kangye ya yi kira ga kwamandojin runduna da su ƙara sa ido tare da wayar da kan jami’ansu dangane da illar haɗa kai da ’yan ta’adda, yana mai cewa irin wannan cin amanar na iya hana nasarar da ake kokarin samu a yaƙin da ake yi da ta’addanci.

A wani farmaki na daban, rundunar sojoji da dakarun haɗin gwiwa sun kai hare-hare masu haɗa da sintiri na yaƙi, samame, da aikin share fage a ƙananan hukumomin Gwoza, Dikwa, Bama, Chibok, Gujba, Geidam da Yunusari.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Yadda Aka Buɗe Makarantar Koyon Wanki Da Guga A Asibitin AKTH 

Next Post

Ziyarar Da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Ya Kai Jihar Katsina, Matashi Dan Gwagwarmaya Ya Caccaki Jagororin Jihar

aksam

aksam

RelatedPosts

Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana neman jami’inta ruwa a jallo
TSARO

Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana neman jami’inta ruwa a jallo

by Khadija Maitaya
July 24, 2026
Peace Corps of Nigeria Ta Yi Bikin Cika Shekaru 28 da Kafuwa
LABARAI

Peace Corps of Nigeria Ta Yi Bikin Cika Shekaru 28 da Kafuwa

by Khadija Maitaya
July 10, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Jerin kamfanin tsaro na Amurka 10 da ‎China Ta Kakaba wa Takunkumi

by Khadija Maitaya
June 22, 2026
Rundunar  Sojin Najeriya Ta Yi Nasarar Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Abubakar Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane
TSARO

Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Nasarar Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Abubakar Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

by aksam
June 16, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Jerin Kadarori 48 da gwamnatin Tarayya ta kowace wa  Tsohon ministan Shari’a Abubakar Makami SAN

Jerin Kadarori 48 da gwamnatin Tarayya ta kowace wa Tsohon ministan Shari’a Abubakar Makami SAN

July 18, 2026
Da Dumi-Dumi: Iran ta fice daga kungiyar (IAEA) ta Duniya

Da Dumi-Dumi: Iran ta fice daga kungiyar (IAEA) ta Duniya

June 23, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

September 7, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media