Rahotanni na nuni da cewa yanzu haka hankalin ‘yan arewa mazauna garin Abavo da ke jihar Delta ya soma kwanciya, biyo bayan janye wa’adin da masarautar garin ta ba su na kwanaki hudu da su fice daga garin, saboda yawaitar matsalar sace-sacen jama’a da ta addabi yankin.
Janye wa’adi na zuwa ne bayan kwarmata lamarin da ‘yan arewa suka yi a kafafen sadarwa, har ya kai ga kunnen fadar shugaban Najeriyar, da gwamnan jihar Delta, da shugaban ƙaramar hukumar Ika ta Kudu, da Haɗakar ƙungiyoyin kare fararen hula na arewacin Najeriya ta CNG, suka shiga tsakani.
Sarkin Hausawan garin na Abavo, Usman Alasan ya shaidawa manema labarai cewar “mun yi sallah lafiya ranar juma’a babu wanda ya ce mana kanzil, gwamnan jihar ya turo mana wakilai don jin halin da muke ciki, sannan aka tura DPO ya je wajen sarakunan yankin, inda kuma ya dawo ya sanar da su cewar an janye wannan wa’adi da aka ba su”
Sarkin Hausawan garin na Abavo ya ce “Dukkan ɓangarorin an yi kira garesu tare da jan hankalinsu da dukkan su su zauna da juna lafiya ba tare da wata fargaba ba” inji shi.








