Haɗakar kungiyoyin da suka mara wa Asiwaju baya yayin yakin neman zaben 2023 ta shiyyar Arewa Maso Yammacin Najeriya sun yi kira ga gwamnatin akan ta gaggauta bincikar ƙaramin ministan tsaron Najeriya Alh Bello Matawallen Maradun
Kungiyoyin sun bukaci gwamnatin tarayya da gaggauta binciken karamin ministan tsaron ne biyo bayan faifan bidiyon da Bello Turji ya sake a kafafen sada zumunta da ke nuni da zargin da ɗan ta’addan dajin nan Bello Turji yayiwa ministan da sunan yana marawa yan ta’addan baya a jihar ta Zamfara.
Haƙiƙa irin wannan zargi da ɗan ta’addan yayiwa tsohon gwamnan jihar Zamfara abune mai girma da yakamata gwamnati ta bincike shi don tabbatar da waɗanda gwamnati za ta sanya a matsayin wakilan ta musamman harkar tsaro.
Hadakar sun bayyana cewa ƙaramin ministan tsaron haka yayi watsi da dukkan kungiyoyin da suka mara musu baya tun bayan kammala zaɓe, wannan ke nuni da cewa halin ko in kulan da ministan ke yi abin takaici ne da tashin hankali, yayin da muke kira da a dakatar da shi a bincike shi har zuwa lokacin da bincike zai tabbatar da ingancin maganganun da akayi.
Jerin kungiyoyin da suka yi wannan kiran:
1- Tinubu Media Team
2- Tinubu Arewa Reporters
3- Jagaban For President Action Group
4- Bola Tinubu Intellectual Coalition
5- Tinubu/Shettima Supporters Worldwide
6- Tinubu Grassroots Movement
7- Bola Tinubu Volunteers Movement
8- Manufa Daya For Tinubu 2023
9- Masoya Katsina Tinubu Da Dikko
10- United Arewa Marketers Association For Asiwaju
11- Arewa For Tinubu Progressive Movement
12- Yobe Trust Asiwaju Movement
13- Northwest Project For Tinubu
14- OOM Support For Asiwaju 2023
15- Tinubu Online Campaign Council










