Yanzu yanzu gwamnatin jihar Kano ta dakatar da katafaren ginin da ake zargin cibiyar harkokin fina fanai ce a Dorayi unguwar bello Dake karamar hukumar Gwale.
Kwamatin karta kwana da Gwamnatin Kano ta Kafa kan kawar da gine gine da aka yi ba bisa ka’ida ba shine ya jagoranci dakatar da ginin.
Kwamatin bisa jagorancin Dakta Dalhatu Aliyu Sani Yace an dakatar da ginin ne biyo bayan korafe korafe daga mazauna yankin na Dorayi.
Yace wurin zai cigaba da kasance wa a dakace har sai abinda hali yayi.
Za a jimu da karin bayani a labarun mu na nan gaba.
COV ASI












