Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya amince da yin cikakken gyara ga tsarin Hukumar Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), inda za a bai wa fararen hula alhakin gudanar da harkokin yau da kullum na hukumar, yayin da jami’an soji za su ci gaba da kula da tsaron masu yi wa ƙasa hidima a faɗin Najeriya.
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa Tinubu ya umarci Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, da Ministan Matasa, Ayodele Olawande, da su yi gyaran dokar NYSC domin ta dace da sabbin sauye-sauyen da aka amince da su, tare da ba da damar fara aiwatar da su nan take.
Daga cikin sauye-sauyen akwai amfani da fasaha wajen kiran masu yi wa ƙasa hidima, tura su zuwa wuraren aiki bisa la’akari da yanayin tsaro, da kuma sake fasalin shirin horaswa na makonni shida.
Haka kuma, an soke faretin kammala bautar ƙasa na gargajiya (Passing Out Parade), inda za a maye gurbinsa da sabon bikin kammala hidima tare da gabatar da sabbin kayan NYSC da za su nuna ƙwarewa da kishin ƙasa.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara ta musamman, Hadiza Bala Usman, ta ce za a raba sansanin horaswar na makonni shida zuwa matakai uku. Makonni na farko da na biyu za su mayar da hankali kan nauyin ɗan ƙasa, ƙimomin ƙasa da haɓaka shugabanci.
A makonni na uku da na huɗu kuma, za a koyar da tsara sana’a, ilimin harkokin kuɗi, dabarun kasuwanci da hanyoyin samun tallafin kuɗi.
Sai makonni na biyar da na shida, waɗanda za a keɓe domin horaswa ta musamman bisa fannin aikin da kowane mai yi wa ƙasa hidima ya zaɓa.
Bugu da ƙari, masu yi wa ƙasa hidima za su riƙa zaɓar ɗaya daga cikin sabbin fannonin horaswa guda 11 yayin yin rajista. Fannonin sun haɗa da: Bangaren Noma, Bangaren Lafiya, Bangaren Ilimi, Bangaren Fasaha da Na’ura Mai Ƙwaƙwalwa, Bangaren Shari’a, Bangaren Ayyukan Gwamnati, Bangaren Ababen More Rayuwa, Bangaren Kare Muhalli, Bangaren Kasuwanci, Bangaren Tattalin Arziki da Ƙirƙira da kuma Bangaren Tsaro.
Hadiza Bala Usman ta bayyana cewa sabbin fannonin za su taimaka wajen bai wa matasa ƙwarewar aiki da ta dace da karatunsu, sha’awarsu ta sana’a da kuma buƙatun ma’aikata a Najeriya, yayin da tura masu yi wa ƙasa hidima zuwa wuraren aiki zai riƙa la’akari da halin tsaro a ƙasar.












