Gwamnatin jihar Kano ta sake daukar mataki kan wasu kungiyoyi da ake zargin suna rajin kare ‘yancin masu auren jinsi a jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba hukumar Hisbah umarnin cafke duk wata kungiya da take tallata auren jinsi a fadin jihar Kano.
Mai tallafawa gwamnan ta fuskar kafofin sada zumunta, Abdullahi I. Ibrahim ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a shafinsa na X.
Abdullahi Ibrahim ya ce:
“Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya umurci hukumar Hisbah da ta cafke kungiyoyin da ake zargi da tallatawa da kuma fafutukar kare hakkin masu auren jinsi a Kano.”
Sanarwar ta ce tallatawa ko kuma kare ‘yancin masu auren jinsi ta hanyar bayyanawa a fili ya saba da dokar jihar Kano.









